Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rudy Juliani Ya Ki Bai Wa Majalisar Wakilan Amurka Hadin Kai


Lauyan Shugaba Trump na kansa, Rudy Juliani, ya yi kememe ya ki mika wasu takardu da Majalisar Wakilan Amurka ta nemi ya mika mata, wadanda ake zargin su na da alaka da yunkurin da ya yi na tursasa Ukraine ta binciki tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden.

Kwamitocin da ‘yan Democrat ke jagaoranta, wadanda ke binciken da mai yiwuwa ya kai ga tsige Trump, sun ba Juliani wa’adin jiya Talata da ya mika takardun, amma abin ya citura, lamarin da ake ganin zai iya sa a tuhume shi da laifin wulakanta majalisar.

A cewar lauyan Juliani, Jon Sale, binciken ba shi da hurumi ko tushe a kundin tsarin mulkin Amurka kuma haramtacce ne.

Ana dai zargin Juliani ne na da hannu dumumu a matsin lambar da aka nunawa Ukraine, kan ta binciki Biden da dansa Hunter Biden.

Masu fashin baki a kasar ta Ukraine irinsu, Serhiy Leshchenko na ganin an saka Ukraine din yanzu haka a tsaka mai wuya, kuma akwai bukatar hukumominta su yi taka-tsantsan

Har ila yau Ya kara da cewa, “ga kasar ta Ukraine, ta bi bangaren ‘yan Republic ne ko Democrat? Abin da ya fi dacewa shi ne, ta zama ‘yar ba ruwanmu.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG