Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rufe Iyakar Mali Da Nijer Ya Tsayar Da Harkokin Sufuri


ECOWAS logo

A jamhuriyar Nijer, masu aikin jigila sun koka a game da tsayawar harakoki bayan da hukumomin sufuri suka rufe iyakar kasar da makwabciyarta kasar Mali.

Sai dai kungiyar ECOWAS ta kakaba takunkumin kan Mali da nufin matsa lamba ga gwamnatin Colonel Assimi Goita don ta gaggauta shirya zaben da zai bada damar maida Mulki a hannun fararen hula.

Motoci masu yawa kirar bus bus na kamfanonin jigilar fasinjoji da manyan motocin dakon kaya ne ke kai da kawo a kowace rana tsakanin kasashen Nijer da Mali, ba’idin tarin motocin hayar da jama’ar kasashen biyu ke amfani da su, sai dai wannan hada hada ta tsaya cik sakamakon matakin ladabtarwar da kungiyar CEDEAO ta dauka akan hukumomin Mali da take zargi da saba alkawalin shirya zabe.

Tuni dai wannan mataki ya fara damun kamfanonin sufuri, kamar yadda shugaban kamfanin Al’izza Transport Mohamed Bakay ya bayyana wa sashen Hausa na Muryar Amurka.

Duk da koma bayan da fannin tattalin arziki ka iya fuskanta sanadiyar wannan mataki ana ganin illolinsa na iya shafar dangantakar al’umomin Mali da makwafta.

To amma, magatakardan ofishin ministan sufuri Attaou Zakawanou na cewa wajibi ne Nijer ta mutunta tsarin bai dayan da kasashen yankin Afrika ta yamma suka cimma saboda haka ya bukaci jama’a su yi hakuri da yanayin da aka shiga a yau.

Koda yake matakin na CEDEAO bai shafi kananan jiragen soja ba, ministan tsaron kasar Nijer Alkassoum Indatou wanne ya yi tunatarwa akan haka ya aike da wasika zuwa ga hukumar kula da filayen jiragen sama, domin sanar da ita cewa a nemi izinin gwamnatin Mali kafin baiwa kowane jirgin da ya tashi daga Nijer damar ratsa samaniyar kasar ta Mali kokuma yada zango, yayin da gwamnatin rikon kwaryar Guinea Conakry ta yi watsi da matsayin na shugabanin kasashen yammacin Afrika.

Ta na mai cewa iyakokin kasar abude suke ga kowa.

XS
SM
MD
LG