Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Borno: An kai harin kunar bakin wake cikin wani gida a Maiduguri


Harin kunar bakin wake cikin wani gida da 'yan kwanakwana suke kokarin kashe gobarar da ta tashi
Harin kunar bakin wake cikin wani gida da 'yan kwanakwana suke kokarin kashe gobarar da ta tashi

‘Yar Kunar Bakin Wake Ta Kai Hari a Wani Gida Rahotanni daga Maiduguri na nuni da cewa, wata ‘yar kunar bakin wake ta tarwatsa kanta ta kashe kimanin mutane goma.

Wannan lamarin dai ya auku ne a daidai lokacin da jami’an tsaro suke gumurzu da ‘yan kungiyar Boko Haram dake kokarin kai hari a Maiduguri. ‘Yan kunar bakin waken ta fake da wannan rudanin ta kutsa cikin gidan mai unguwar tana ambaton sunan Boko Haram kamar tana neman mafaka. Jin haka yasa iyalin gidan duk suka fito tsakar gida domin ganin abinda ke faruwa. Nan take kuma ta tada nakiyar da tayi damar da ita ta kashe matan dagacin uku da ‘yayanshi.

Bisa ga rahoton, mai unguwar ya tsallake rijiya da baya ne sabili da baya gida lokacin da aka kai harin, sai dai ya sake auna arziki jin kadan bayan harin na farko inda ‘yar kunar bakin wake ta biyu da tarwatsa kanta a kofar gidan inda jama’a suka taru suna kokarin kai dauki.

Wannan harin ya auku ne jim kadan bayanda gwamnan jihar Borno Kashim Shattima ya wakilci shugaba Muhammadu Buhari wajen wajen kai ziyara sansannan ‘yan gudun hijira.

Ga rahoton da wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda Bi’u ya aiko daga Maiduguri, jihar Borno.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:34 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG