Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Wasu Mutane Da Ake Zargi Da Safarar Jarirai A Adamawa


Sojojin Najeriya a wani aikin sintiri da suka yi (Facebook/ Nigerian Army)
Sojojin Najeriya a wani aikin sintiri da suka yi (Facebook/ Nigerian Army)

Rundunanr Sojojin Najeriya ta gabatar wa manema labarai wasu mutane 26, cikin su mata 17 da maza 7 da ake zargi da laifin safarar jarirai a jihar Adamawa da ke Arewa maso gabashin kasar.

ADAMAWA, NIGERIA - Ana zargin mutanen ne da safarar jariran da matan ke haifa suna sayarwa a yankin iyakar Najeriya da Jamhuriyar Kamaru, a Belel na karamar hukumar Maiha da ke jihar Adamawa.

Shugaban Bataliya ta 33 ta Rundunan Sojojin Najeriya a jihar Adamawa Manjo Janar Muhammad Jibrin Gambo ne ya tabbatar da hakan a barikin Sojoji na Gepson Jalo.

Yayin da ya ke jawabi wa manema labarai, shugaban sojojin ya ce sun samu wannan nasara ne ta hanyar bayanan sirri da suke samu tare da hadin gwiwa da suka yi da jami’an tsaron farin kaya wato DSS.

Daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Gambo Musa wanda ‘dan jihar Adamawa ne daga karamar hukumar Mubi ta kudu, ya ce wannan batun da ake zargin su da shi ba haka bane, su ‘yan rawa ne kawai basu da wata alaka da abin da ake zargin su da shi.

Ita ma wata da ake zargin da yin wannan aiki na safarar jariran a yankin Belel da ke karamar hukumar Maiha a nan jihar Adamawa wadda ainihi ta fito daga jihar Gombe da ta bukaci da a sakaye sunan ta, ta yi na’am da zargin ta kuma kara da cewa ita ‘yar rawa ce kuma wani mutum ne ya kawo ta har zuwa yankin na Belel a kusa da kasar ta Kamaru

Saurari cikakken rahotio daga Lado Salisu Garba:

Rundunar Sojin Jihar Adamawa Ta Cafke Wasu Mutane Da Ake Zargi Da Safarar Jarirai.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

XS
SM
MD
LG