Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Fadakar Da ‘Yan Jarida Kan Muhimmancin Bayanan Tsaro


Manyan Hafsohin Sojan Saman Najeriya
Manyan Hafsohin Sojan Saman Najeriya

Rundunar sojin saman Najeriya ta shirya taron bita na musamman ga ‘yan jaridar dake bada rahotannin tsaro a kasar, kan yadda zasu hada rahotannin tsaro tare da kaucewa haddasa fitina.

Yayin da yake jawabi a taron bitar, babban hafsan hafsohin mayakan sama Air Mashal Sadiq Abubakar, ya ce samar da rahotannin tsaro abu ne mai matukar muhimmanci don ci gaban ‘kasa a wannan lokaci, kuma ta hanyar da ake sarrafa shi ta sigar labarai ka iya shafar sha’anin tsaron kasar ta hanyar da zai yiwa kasa kyau ko kuma ya illa.

Taron bitar ya nuni da cewa dole ‘yan jaridun dake hada rahotannin tsaro su fahimci muhimman al’amuran dake tattare da bangaren tsaro, don basu damar gudanar da ayyukansu bisa tsari da kwarewa.

Hadakar Hafsoshin Sojojin Sama da Yan Jaridu Bayan Wani Taron Bita
Hadakar Hafsoshin Sojojin Sama da Yan Jaridu Bayan Wani Taron Bita

Tun da farko cikin jawabinsa kakakin rundunar sojan saman Najeriya, Olatokunbo Adesanya, ya ce makasudin wannan taron bitar shine ana son samar da kwarewa ta musamman ga ‘yan jaridun dake dauko rahotannin tsaro.

Rundunar sojan saman Najeriya ta yi fatan cewa ‘yan jaridu ba zasu bari ‘yan ta’adda su yi amfani da su ba, ta hanyar yada profaganda. Yayin taron an ilimantar da ‘yan jaridu kan nau’o’in jiragen yakin Najeriya da ire-iren makaman rundunar sojan saman kasar, har ma da shirye-shiryen da ake kafin akai kowanne irin hari.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:09 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG