Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Kori Tsohon Mukaddashin Shugaban Hukumar NIA Daga Aiki


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Kama daga majalisar wakilan Najeriya da masu fafutikar kare hakkin dan Adam a Najeriya tamkar kowa na cikin rudani a kan badakalar dake faruwa a hukumar leken asirin kasashen waje, NIA inda yanzu gwamnatin Buhari ta sallami tsohon mukaddashin shugsbsn hukumsr daga aiki

Bayanai daga hedkwatar hukumar leken asirin kasashen waje ta Najeriya, wato, NIA, na cewa gwamnatin shugaba Buhari ta kori Ambasa Muhammad Dauda, tsohon mukaddashin shugaban hukumar, daga aiki, wanda kwanaki biyu da suka gabata jami'an DSS suka yi wa gidansa kawanya.

Korar na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar wakilai ke binciken wata badakalar zunzurutun kudi na dalar Amurka miliyan 289 da kuma cancanta ko rashin cancantar nadin Malam Ahmed Rufai a matsayin shugaban hukumar ta NIA.

A hirar da Muryar Amurka ta yi akan abubuwan dake faruwa da Hajiya Naja'atu Muhammad, jami'ar daya daga cikin kungiyoyin dake kare hakkin bil Adama a Najeriya, ta bayyana cewa abun da aka yi abun kunya ne kuma ya kada ta. Ta ce shi Ambasa Muhammad Dauda ya na aikinsa aka nada wani dabam ba tare da samunsa da wani laifi ba. Amma sai ga shi gwamnatin Buhari ta kore shi daga aiki ma gaba daya.

Hajiya Naja'atu ta ce bugu da kari sai ga shi Shugaba Buhari ya nada wani kwamitin bincike a karkashin shugabanci Babagana Kingibe wanda ake zarginsa da yi da sama da fadi da miliyoyin dala.

Yayin da Majalisar wakilai ta fara bincike shi Muhammad Dauda ya fada ya ba Babagana Kingibe wasu kudi kuma akwai sauran kudi fiye da dala miliyan arba'in. Muhammad Dauda ya ce za'a yi sama da fadi da kudin saboda haka sai ya kai kara. Bugu da kari sai gwamnati ta nada wanda majalisa ta ce kada a nada a matsayin shugaban hukumar.

Shi ko Aminu Sani Jaji, shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilan Najeriya, wanda kwamitinsa ke gudanar da bincike akan badakalar NIA din, ya ce yana bukatar lokaci domin ya gudanar da bincike kafin ya yi magana.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG