Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojojin Saman Najeriya Ta Ce Tana Jiran Umarnin Tinubu Don Cika Aiki


Rundunar sojojin saman Najeriya.
Rundunar sojojin saman Najeriya.

Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce ta shirya tsaf don cika duk wani umarni da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai ba su na cika aiki.

Babban hafsan Hafsoshin rundunar mayakan saman Kasar, Air Marshall Hassan Bala Abubakar ke bayyana hakan a wani babban taro da ya yi da dukan kwamandojin rundunar.

Air Marshal HB Abubakar ya ce rundunar za ta ci gaba da mika wuya da yin biyayya ga shugannin fararen hula a kowane lokaci, sannan za ta ci gaba da zama cikin shirin ko ta kwana.

Babban hafsan Hafsoshin rundunar mayakan saman Kasar, Air Marshall Hassan Bala Abubakar
Babban hafsan Hafsoshin rundunar mayakan saman Kasar, Air Marshall Hassan Bala Abubakar

Babban hafsan hafsoshin mayakan saman Najeriyar ya yi bayanin cewa yanzu haka abin da ke faruwa a Najeriya da ma makwabtanta a Afirka ta yamma wani sha'ani ne mai sarkakiya da ka iya tasiri kan yanayin siyasar yankin.

Rundunar mayakan saman Najeriya
Rundunar mayakan saman Najeriya

Wannan dai duka na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ECOWAS ke baiwa dakarun kasashen umarni su zauna cikin shiri don afkawa kasar Nijar da nufin maido da demokradiyya muddin sojojin juyin mulkin suka ci gaba da bijirewa ka'idoji da sharuddan da aka gindaya masu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG