Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Yaki Da ‘Yan Ta’adda A Jihar Filato Ta Halaka Wasu Bata Gari Da Ta Fatattaka


Rundunar dake yaki da ‘yan ta’adda a jihar Filato OPERATION SAFE
Rundunar dake yaki da ‘yan ta’adda a jihar Filato OPERATION SAFE

Wata sanarwa da rundunar da ke wanzar da tsaro a jihar Filato, Operation Safe Haven ta aikewa manema labarai ta bakin kakakinta, Captain Oya James, na nuni da cewa, rundunar ta sami kiran gaggawa daga wadansu da ‘yan bindigar suka yi musu kwanton bauna a hanyar Mangu zuwa Pushit.

PLATEAU, NIGERIA - Sanarwar ta ce cikin hanzari dakarun suka kai dauki suka kuma cimma ‘yan ta’addan, inda suka halaka uku daga cikinsu tare da kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku da harsasai guda goma sha hudu da babur guda daya da katin shaidar ‘yan sanda mai matakin kurtu, yayinda wassu daga cikinsu suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Kwamandan Operation Safe Haven, Manjo Janar Abdulsalam, Rundunar dake yaki da ‘yan ta’adda a Jihar Filato
Kwamandan Operation Safe Haven, Manjo Janar Abdulsalam, Rundunar dake yaki da ‘yan ta’adda a Jihar Filato

Sanarwar ta kara da cewa kwamandan Operation Safe Haven, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar ya jaddada cewa ,rundunar zata ci gaba da jajircewa wajen gudanar da aikinta bil hakki da gaskiya.

Wannan nasara da rundunar sojin suka yi na zuwa ne kwana guda bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su nemo masu aikata kisan al’umma a jihohin Filato da Binuwai.

A cikin sanarwar daga hadiminsa, Dele Alake, shugaban Tinubu ya bayyana takaicinsa yadda ake kisan mutane, ciki har da kananan yara.

Wasu bindigogi da aka kwato daga hannun ‘yan ta’adda
Wasu bindigogi da aka kwato daga hannun ‘yan ta’adda

Gwamnan Jahar Filato, Barista Caleb Mutfwang yayi fatar samun hadin kai daga mabambantan addinai da kabilu a jihar.

Al’ummar karamar Hukumar Mangu a cikin ‘yan kwanakin nan sun sha fama da hare-haren ‘yan bindiga inda aka kashe mutane da dama, dubban jama’a na gudun hijira cikin sanyi da ruwan sama da rashin abinci da cututtuka musamman a tsakanin kananan yara.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:

Rundunar Yaki Da ‘Yan Ta’adda A Jihar Filato Ta Halaka Wasu Bata Gari Da Ta Fatattaka.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG