Rundunar tace duk wanda ta samu yana tursasawa jama'a to idan ya shiga hannu ya kwana da sanin cewa ya debo ruwan dafa kansa ne. Mataimakin sifeton 'yan sanda Mamman Ibrahim Tsafe shi ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da manema labarai.
Duk da yake suna neman karin albashi amma sifeto janaral nasu na iya bakin kokarinsa domin samarda wasu abubuwan jin dadi da ka karawa 'yan sandan kwarin gwiwa. Yayin da rundunar ke kokarin yin abubuwan da ka iya sa su ji dadin ayyukansu amma kuma duk wanda ya taka doka ya gama yawo. Babu inda za shi.
An roki jama'a su saki jiki su dinga ba manyan jami'an 'yan sanda bayanai akan wadanda suke aikata ayyukan asha ko da ma jami'an 'yan sanda ne.
Ga karin bayani.