Accessibility links

'Yansanda Sun Kashe 'Yan Fashi da Makamai su Hudu Bayan Musayar Wuta

  • Aliyu Imam

Wasu 'yan sandan Nijeriya a bakin aiki

Kwamishinan Yansandan jihar Alhaji Abdulkadiri Indabawa ne ya bayyana a wani taron manema labarai inda ya gwada musu gawarwakin 'yan fashi da makaman.

Rundunar ‘Yansandan Najeriya a jihar Oyo dake yammacin kasar ta bada labarin ta kashe ‘yan fashi da makamai su hudu.

Kwamishinan ‘Yansandan jihar Alhaji Mohammadu Abdulkadiri Indabawa ne ya bayyana haka lokacinda yake gwadawa manema labarai gawarwakin ‘yan fashin da suka halaka, a taron manema labarai d a ya kira ofishin rundunar dake Badun babban birnin jihar ta Oyo.

Daga nan kwamishinan ya roki jama'a su taimakawa hukumar da bayanai da zasu taimaka wajen kama mabarnata.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG