Accessibility links

Rundunar 'Yansandan Adamawa Zata Tabbatar An Gudanae da Zabe Koina a Jihar


Wasu 'yan gudun hijira a Adamawa

Rundunar 'yansandan tace ta shirya ta gani an gudanar da zabe koina har da sansanin 'yan gudun hijira.

A wurin taron masu ruwa da tsaki da rundunar ta gudanar da shugabannin jam'iyyu a jihar kwamishanan 'yansandan yace sun shiryawa zaben.

Mr. Adabi Gabriel kwamishanan 'yansandan yace batun gudanar da zabe a arewacin jihar ba nasu ba ne amma na hukumar zabe. Hakin da ya rataya akansu shi ne su shirya su tabbatar da tsaro lokacin zaben. Akan wannan sun shirya tsaf.

Taron na zuwa ne yayin da gwamnan jihar ke cigaba da kiran a dage zaben duk da cewa shi ne jam'iyyarsa ta PDP ta baiwa kujerar takarar zuwa majalisar dattawa. Gwamnan ya hakikance cewa bai kamata a gudanar da zabe a yanayin da ake ciki. Yace mutanensu da dama na gudun hijira. Maimakon zabe kamata yayi a nuna alhini kan lamarin da jama'a ke ciki.

Amma al'ummomin da rikici ya rabasu da gidajensu sun ce duk da cewa ba dadi suke ji ba sun shirya su shiga zaben. Mr. Adamu Kamale wanda yake wakiltar wata mazabar Michika yankin da yanzu yake hannun 'yan Boko Haram ya bayyana irin damarar da suka yi game da zaben. Yace dole su yi tunanen gaba. Idan basu yi zabe ba to kenan basa cikin Najeriya. Yace basu da wata kasa sabili da haka duk da matsalar da suke ciki zasu fita su yi zabe.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

XS
SM
MD
LG