Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda A Abuja Sun Kubutar Da Mutane 58 Da Ake Garkuwa Dasu

Rundunar Yansandan Babban Birnin Abuja Bayan Wani Barin Wuta A Cikin Daji Ta Sami Nasarar Kubutar Da Mutane 58 Da Ake Garkuwa Dasu
Rundunar Yansandan Babban Birnin Abuja Bayan Wani Barin Wuta A Cikin Daji Ta Sami Nasarar Kubutar Da Mutane 58 Da Ake Garkuwa Dasu

Rundunar 'yan sandan yankin babban birnin Tarayyar Najeriya ta ce jami'anta sun kai wani samame a cikin dajin Udulu da ke karamar hukumar Gegu a jihar kogi da ke makwabtaka da dajin Sardauna na jihar Nassarawa da dukkanninsu ke makwabtaka da yankin babban birnin Tarayyar.

Kakakin Rundunar 'yan sandan na Abuja SP Josephine Adeh tace Zaratan jami'an 'yansandan sun afka cikin dajin in da bayan da miyagun suka hango su suka bude masu wuta, ta ce kuma 'yan sandan sun maida martani, har suka fi karfin yan bindigar wadanda suka ranta a cikin na kare da raunukan harsasai.

Daga bisani 'yan sandan sun ceto kimanin mutane hamsin da takwas daga sansanin masu garkuwa da mutanen, ko da yake wani mutum daya daga cikin wadanda ake garkuwa da su din ya rasa ransa, biyo bayan musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da yan bindigar.

Rundunar Yansandan Babban Birnin Abuja Bayan Wani Barin Wuta A Cikin Daji Ta Sami Nasarar Kubutar Da Mutane 58 Da Ake Garkuwa Dasu
Rundunar Yansandan Babban Birnin Abuja Bayan Wani Barin Wuta A Cikin Daji Ta Sami Nasarar Kubutar Da Mutane 58 Da Ake Garkuwa Dasu

Masu bincikie kan sha'anin tsaro irinsu Dr Kabiru Adamu na ganin an baro shiri tun rani, kasancewar tun tuni aka cimma wani shirin sintirin samar da tsaro tsakanin dukkannin jami'an tsaron dake jihohi bakwai masu makwabtaka da Abuja, amma har yanzu da sauran rina a kaba.

A bangare daya kuma, masanin tsaro Dr, Abubakar MS na ganin duk da yake 'yan sandan sun cancanci yabo, to amma duk da haka bai kamata ana yin saku-saku da batun tsaro a yankin babban birnin tarayya ba, duba da ita ce cibiyar kasa.

Rundunar 'yan sandan dai ta ce yanzu za ta canza salon tsarin yadda take tunkarar kalubalen tsaro a birnin, ta yadda za ta kai samame har sansanonin 'yan ta'addan ta yadda za'a hana su sakat.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00
XS
SM
MD
LG