Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Sabbin Jiragen Yakin Sojin Sama A Najeriya


Bikin kaddamar da jiragen sama
Bikin kaddamar da jiragen sama

A ci gaba da jaddada matakan tsaro a Najeriya, rundunar sojin kasar ta kaddamar da wasu jiragen da ta sayo daga kasar China.

An kawo karshen bikin cika shekaru hamsin da hudu da kafa rundunar sojin saman Najeriya wanda Ministan tsaro, Mansur Dan Ali ya wakilci Shugaba Buhari inda ya kaddamar da sabbin jiragen yaki samfurin MI35 da aka sayo daga kasar Rasha.

Ya bayyana yadda Shugaba Buhari ya yaba wa rundunar sojin saman bisa rawar gani da suka taka wajen karya lagon mayakan Boko Haram a yankin Arewa maso gabas.

A jawabinsa babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya, Air Marshall Sadiq Baba Abubakar, ya tabo irin gumurzun da sojojin saman su ka yi a lokacin yakin basasar Najeriya da ma Irin rawar da su ka taka a lokacin yakin basasar kasashen laberiya da Saliyo. Baya ga irin yadda suke bada gudunmmuwa wajen samar da tsaro a cikin gida.

Baya ga kaddamar da sabbin jarigen yakin yayin wannan biki, an kuma kaddamar da sabbin rundunoni biyu na sojin saman wanda a yanzu rundunoni takwas sojojin saman Najeriyar ke da su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG