Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabbin 'Yan Majalisun Venezuela Da Aka Zaba Sun Fara Aiki


hotan shugabannin 'yan adawar Venezuela.
hotan shugabannin 'yan adawar Venezuela.

'Yan Majalisun da aka zaba a kasar Venezuela domin gyara ga kundin tsarin mulkin kasar sun fara aiki, duk kuwa da korafin da ake kan zaben na su.

A yau Juma’a Majalisar nazarin kundin tsarin mulkin kasar Venezuela ta soma taronta na farko a zauren Majalisar dake birnin Caracas, duk da korafin kasashen duniya da kuma zanga-zangar ‘yan masu adawa.

Zaman‘Yan Majalisar su 545 da aka zaba su sake nazarin kudin tsarin mulkin kasar Venezuela zai iya janyo takun saka tsakanin shugaban kasa Nicolas Maduro da ‘yan jam’iyyar adawa, wadanda suka ce ba a yi adalci a yadda aka zabo wakilan.

Wata mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Heather Nauert, tace Amurka ba ta amince da nadin ‘yan Majalisar ba, ta kara da cewa babu inganci a zaben tunda bai samu kulawar masu nazarin zaben na kasa-da-kasa ba.

Nauert, ta ce Amurka na kallon Majalisar ne a matsayin gungun wasu da aka zaba domin su taimakawa Maduro wajen ci gaba da gudanar da mulkin kama karya, wanda batanci ne ga akidar dimokaradiyya.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG