Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Babi A Majalisar Dokokin Kasa


Mutan Najeriya na haramar bukukuwan rantsar da Shugaban Kasa, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, Mayu 28, 2015.

Makon nan mai zuwa ne za a bude sabon babi a siyasar najeriya, domin za’a rantsar da sabon majalisa ta karni na takwas, amma kuma har yanzu dambarwar wanene zai zama shugaba a majalisar dattawa ko kuma kakakin majalisar wakilai tana kasa tana dabo, shin chanchanta za a bi ne ko sababbi masu rinjaye za su yi nasarar chanja tsarin majalisar da aka dade ana amfani da su.

Takaddamar da ta kunno kai a yanzu tsakanin tsofaffin ‘yan majalisar da sababbi, a game da manyan mukamai kamar na kakakin majilisar wakilai da kuma na shugaban majalisar dattawa, sababbin ‘yan majalisar dake da rinjaye a majalisar dokokin na ganin an canja tsarin mulkin majalisar da aka dade ana amfani da shi, wanda ya samo asali tun da aka fara mulkin farar hula a Najeriya.

‘yar majalisar wakilai kuma wadda ta sake samun nasarar lashe zabe a bana Khadija Bukar Abba Ibrahim, tace, “akwai dokoki da suka ce sababbi ‘yan majalisa na dokoki dana wakilai ba zasu iya takarar wasu mukamai ba,” wanan wani tsarin kuduri ne na majalisar wanda ya dade ana aiki da shi a kasar.

Kodayake a cikin ‘yan jam’iyyar APC masu rinjaye akwai masu goyon bayan sabbin da suyi hakuri, su baiwa wanda suka kware dama. Injiniya Yunusa Ahmed Abubakar, sabon ‘dan majalisar wakilai ne daga jihar Gombe kuma yana daga cikin masu wannan tunanin, inda yace, “Mu muyi hakuri sabbi da muka shigo, idan bamu baiwa masu kware wa a kai yi ba to gaba in muka dawo zamu ga muhimmancin kwarewar.”

Aikin majalisa dai ba’a koyar dashi a wata makaranta ko jami’a, dole ne abakin aiki ake koyarsa har a kware.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG