Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Binciken Jin Ra'ayin Amurkawa Kan Siyasar Amurka


Wani sabon binciken jin ra’ayin Amurkawa da aka fitar da sakamakons a yau Litinin, ya nuna cewa, Amurkawa sun fi duba yiwuwar jefawa dan takarar Democrat, Bernie Sanders kuri’a, fiye da kowane dantakara da ya rage a yakin neman zaben 2016.

Binciken jin ra’ayin da kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya gudanar, ya ji ra’ayoyin mutane 1,076 a tsakanin watan Maris da Aprilu.

Kuma kashi 21, sun ce lallai Sanders za su jefawa kuri’a, yayin da kashi 41 suka ce akwai yiwuwar duba zabin na Sanders.

Ita dai Hillary Clinton da ta fi samun karbuwa a jam’iyar ta Democrat, ta zo ta biyu a binciken, yayin da a bangaren Republican Ted Cruz da John Kasick duka suka samu kashi 43 a bangarori biyu, sannan Donald Trump ya zo na karshe da kashi 35 a bangarori biyu da aka ji ra’ayin mutanen.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG