Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Gwamnan Jihar Gwambe Zai Yaki 'Yan Kalare


Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan.

Sabon Gwamnan Jihar Gwambe,Alhaji Muhammadu Hassan Dankwambo, ya tabbatarwa al'umar jihar cewa zai kawarda 'yan Kalare cikin jihar.

Sabon Gwamnan Jihar Gwambe Zai Yaki 'Yan Kalar

Sabon gwamnan jihar Gwambe, Alhaji Muhammadu Hassan Dankwambo, ya tabbatarwa al'umar jiharsa cewa zai kawar da ayyukan ta'ddanci da matsan jihar suke yi, wa danda aka fi sani da sunan "kalare.

A hirarsa ta farko da manema labarai, Alhaji Dankwambo yace matsalar matasan nan tana daga cikin manyan matsaloli dake damun mutanen jihar. Yace kawar da matsalar ba mutanen jihar ce kadai zasu amfana ba,har da baki da suke da nufin zuwa jihar domin zuba jari da wasu bukatu.

Gwamna Dankwambo yace, "matsala idan ta riga ta faru babu wanda yake da maganinta sai dai niyya. Gwamnan yace zasu kafa kwamiti na kwararru 'yan jihar, dake ciki da waje su zo, haka suma matasan za'a gayyace su su zo domin a gano shin wan nan matsala kam ina asalinta ne.

XS
SM
MD
LG