Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Matsayin Majalisar Dattawan Najeriya Kan Dokar Zabe


taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade
taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade

Kafin wannan matakin, majalisar dattawan ta ki amincewa da yin amfani da yanar gizo wajen aikawa da sakamakon zabe.

Majalisar Dattawan ta sake duba kudurin yi wa dokar za6e garambawul inda ta ba Hukumar za6e mai zaman kanta wuka da nama sa6anin matakin da ta dauka watanni uku da suka wuce . A yanzu Hukumar ce za ta za6i hanyar da ta dace wajen aikawa da sakamakon zabe ko ta yanar gizo wato intanet ko kuma da takarda da aka rubuta sakamakon da biro.

majalisar-dattawan-najeriya-za-ta-yi-bitar-sabuwar-dokar-zabe

takaddamar-da-ta-faru-a-majalisar-dattawa-kan-dokar-zabe

zaben-gwamnan-jihar-anambra-na-fuskantar-barazana---inec

A cikin hirarshi da Muryar Amurka, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya Shugaban Komitin Kula da Hukumar Za6e a Majalisar Dattawan ya bayyana cewa, tun farko sun amince da amfani da na'ura wajen gudanar da zavem sau dau avubda va sy tarda da sgu vatattara sakamakon zabe, abinda ba su yarda da shi ba da farko shine a turo da sakamakon zabe ta yanar gizo saboda wadansu za su iya yin amfani da dabaru wajen sauya sakamakon zaben.

Daya cikin 'ya'yan majalisar dattawan wanda aka yi gyaran dokar da shi kuma Sanata Mai wakiltan Jihar Kebbi ta tsakiya, Mohammed Adamu Aliero ya yi karin bayani akan abinda dokar ta kunsa. Bisa ga cewarshi, nan gaba dukan zabukan da za a gudanar za a yi ne ta hanyar zaben dan tinke, ko kuma kato-bayan-kato yadda ba za a ja ra'ayin wani ta wata hanya ba.

Farfesa Mahmoud Yakubu Shugaban hukumar zaben Najeriya
Farfesa Mahmoud Yakubu Shugaban hukumar zaben Najeriya

Aikin da ya rage yanzu shi ne kwamitin daidaito da ya kunshi mutum 14 daga zauren Majalisun biyu a karkashin jagorancin Shugaban Masu rinjaye Sanata Yahaya Abdullahi Abubakar zai sake duba dokar dalla-dalla, sannan a aikawa Shugaban Kasa Mohammadu Buhari ya ratta6a hannu.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:

Sabon Matsayin Majalisar Dattawan Najeriya Kan Dokar Zabe-3:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG