Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddamar Da Ta Faru A Majalisar Dattawa Kan Dokar Zabe


Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan

Majalisar Dattwan Najeriya, ta ki amincewa a bar wa hukumar zabe ta INEC karfin ikon aika sakamakon zabe ta hanyar yanar gizo.

A maimakon haka, majalisar ta amince cewa, majalisar dokokin kasar da hukumar kula da kamfanonin sadarwa ta NCC ne za su yanke hukunci kan ko a yi amfani da hanyar yanar gizo wajen aika sakamakon zabe ko akasin haka.

Sanatoci 52 ne suka aminta da wannan matsaya yayin da 28 suka nuna adawa. Sanatoci 28 kuma ba su halarci zaman ba.

Wannan gyara da aka yi ya shafi kashi 52 karamin kashi na 3 ne.

Sai dai wani abu da ya dauki hankali a lokacin da ake muhawara akan wannan dokar ita ce batun irin karfin fasahar sadarwa ta zamani wato internet da ake amfani da ita a kasar.

Wasu sun ce kashi 43 na kasar ne ke da karfin fasahar sadarwa ta internet, sanan kashi 57 kuma ba su da fasahar sadarwa mai karfi da za a iya amfani da shi wajen tattara sakamakon za6e a kasar.

Hakan ya sa mataimakin mai tsawatarwa na bangaren marasa rinjaye a Majalisar Dattawan Sanata Ibrahim Danbaba Abdullahi ya yi tsokaci akai yana cewa, an aiko masa da takarada da ke cewa Kashi 98 na Najeriya tana da Karfin fasahar 2G.

Saboda haka idan an yi amfani da na'ura mai aiki da fasahar 2G za a iya tattara sakamakon za6e cikin sauki a lokutan za6e a cewar shi.

Amma Sanata Danbaba ya kara da cewa shi ya kada kuri'arsa da tunanin jamiyarsa ta PDP a zuciya, amma da aka rinjaye su da mafi yawan kuri'u sai ya hakura ya amince da abin da Majalisar ta amince da shi.

Tun shekara 2018 ne dai Majalisa ta takwas ta yi gyara akan dokar za6en nan har sau 3 amma Shugaba Mohammadu Buhari ya ki amincewa da ita.

Abin jira a gani shi ne ko a wannan karon, dokar za ta samu ta tsallaka siradi.

XS
SM
MD
LG