Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Tsarin Biyan Kudi a Tashar Jiragen Ruwan Zai Hana Sata


캄보디아 프놈펜 외곽에서 한 인력거 운전수가 승객을 싣고 도심으로 향하고 있다.
캄보디아 프놈펜 외곽에서 한 인력거 운전수가 승객을 싣고 도심으로 향하고 있다.

A kokarin dakile kwange da yawan sace-sace hukumar tashar jiragen ruwan Najeriya ta fito da wani sabon shiri

Domin dakile hanyar da ake bi ana yiwa hukumar tashar jiragen ruwa kwangen kudin shiga hukumar ta fito da wani sabon tsari.

Hukumar ta shirya taron fahimtar juna tsakaninta da masu muamalar kudi da ita domin sanarda su yadda wannan sabon shirin zai yi aiki. Da yake jawabi a wurin taron shugaban hukumar tashar jiragen ruwan Najeriya Alhaji Habibu Abdullahi yace bayan toshe kurarar kudi ba bisa ka'ida ba haka sabon shirin zai sa harkokin biyan kudi ga hukumar ya kara sauri. Yace yana fata da sabon shirin ya fara aiki biyan kudin da ake yi har na tsawon sati guda ya koma na 'yan mintoci kadan. Yace maimakon mutane suna zuwa ofisoshinsu suna biyan kudi to yanzu zasu biya ne a bankuna kuma da sun biya maimakon su jira har sai kwana uku ko biyar su samu tabbaci sabon tsarin zai sa cikin 'yan mintuna zasu sani.

Kodayake shugaban hukumar yace ana yi masu kwangen kudi amma yace sai sun fara sabon tsarin zasu san irin asarar da suka yi can baya. Amma yace babu shakka akwai kwangen musamman a harkar kasuwanci.

Wani Mr Kehinde Alao dake hulda da hukumar yace sabon tsarin zai rage masu bata lokaci da suke yi wajen biyan kudi kafin su fitar da kayansu daga tashar jiragen. Ban da haka sabon shirin zai rage kashe kudade. Shi ma Malam Nasidi yace sabon tsarin zai rage raguwar sace-sacen kudi da magudi da rage yawan jeka ka dawo.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG