Accessibility links

Kungiyar Matan Borno ta Kira Gwamnatin Tarayya ta Tallafa Masu


Mata suna kokarin tsrewa daga hare-hare

Mata da yara su ne hare-haren da 'yanbindiga ke kaiwa jihar Borno ya fi shafa domin ana kashe masu mazajensu da 'ya'yansu maza matsa kana a kone masu muhallansu da gonakai.

Kungiyar matan jihar Borno ta koka da irin ukubar da suke sha sanadiyar yawan hare-haren da 'yanbindiga ke kaiwa jihar inda ake kashe masu mazajensu lamarin da ya sa dole su bar muhallansu.

Kungiayr ta kira gwamnatin tarayya da ta kawo doki ga mata da yara wadanda suka tagayyara sakamakon hare-haren da jihar ke fama da su.Shugabar kungiyar Aishatu Liman tace gwamnatin jihar kadai ba zata iya daukan duk nauyin mata da yara da hare-haren suka shafa ba. Shugabar tace lokaci yayi da gwamnatin tarayya ya kamata ta waiwayosu domin irin halin da suke ciki a jihar.

Abubuwan da suke faruwa inji shugabar sun fi karfinsu. Kashe iyaye maza da ake yi ya sa mata da yara cikin mummunar wahala. Tace gwamnan Borno Shettima yayi nashi kokarin. Yana bada taimkon kudi ,ya kai ziyara wani zibin ma ya yi kuka ganin irin halin da al'ummarsa ta shiga. Tace gaskiya abubuwan sun yiwa gwamnan yawa. Ta roki shugaban kasa da babbar murya da ya fito ya tallafwa mata da yaran jihar da hare-haren suka rutsa da su. Mazajensu suna mutuwa ko ta ina dare da rana.

Kiran da kungiyar ta yi bai tsaya kan shugaban kasa ba da gwamnatin tarayya kawai ta kira majalisun kasa da su tashi su taimakesu musamman yaran da suka zama marayun dole. Gwamnan jihar da Sanata Ali Ndume su ne kadai suke taimakawa mutanen dake cikin muguwar wahala.

XS
SM
MD
LG