Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Tsarin Biyan Ma’aikata Rabin Albashinsu A Jihar Niger Bai Samu Karbuwa Ba


Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello

Majalisar Dokokin jihar Niger tayi Allah wadai da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na biyan rabin albashin ma’aikatan gwamnatin jihar a dai dai wannan lokaci.

A wani taron manema labarai da shugaban kwamitin kula da harkokin ma’aikata na majalisar ya kira Abdul Malik Boso, yace majalisar ba ta gamsu da wannan mataki ba kuma bata yarda da hujjojin gwamnatin jihar Niger ba, na cewa rashin kudi ne yasa aka biya ma’aikatan rabin albashinsu.

Shima shugaban marasa rinjaye na Majalisar Bello Agwara, ya tabbatar da matsayin majalisar kan wannan batu, inda yace hakki ya rataya ga gwamnati wajen tsayawa dubi hanyar da zata sami kudi ta biya ma’aikatanta.

A halin da ake ciki dai kungiyar kwadagon jihar ta ja daga, har ta fara raba takardun cewa zata fara wani yajin aiki mai zafi daga ranar Litinin mai zuwa, har sai gwamnatin jihar ta janye sabon tsari na biyan ma’aikata rabin albashinsu.

Saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG