Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Guguwa A PDP; Gwamnoni Sun Nemi A Maida Wuka Kube


Gwamnonin PDP Sun Yi Taro A Makurdi
Gwamnonin PDP Sun Yi Taro A Makurdi

Wata sabuwar dambarwa ta kunno kai a babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, sakamakon murabus da wasu shugabannin jam’iyyar 7 na kasa suka yi daga mukamansu.

Gwamnonin jam’iyyar PDP a Najeriya sun yi kira ga daukacin ‘yan jam’iyyar a duk fadin kasar, da su kwantar da hankalinsu dangane da guguwar da ta taso a cikin jam’iyyar, inda wasu shugabannin 7 na kasa suka gabatar da takardunsu na yi murabus daga mukamansu.

Wata sanarwa da shugaban gwamnonin na PDP kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya fitar, ta ce ana nan ana kokarin samo bakin zaren warware wannan takaddama da ta kunno kai.

Gwamnonin PDP a wani taro da suka yi kwanan nan (Twitter/ PDP)
Gwamnonin PDP a wani taro da suka yi kwanan nan (Twitter/ PDP)

A jiya Talata ne dai shugabannin 7 suka mika takardunsu na yin murabus, saboda zargin an maida su saniyar ware, da kuma zargin shugaban jam’iyyar na kasa Uche Secondus, da kasawa wajen hada kan shugabanni da membobin jam’iyyar domin ci gaban lamurranta.

Shugabannin da suka yi murabus din sune mataimakin sakataren watsa labarai na kasa Diran Odeyemi; mataimakin mai ba da shawara kan sha’anin shari’a Ahmed Bello; Mataimakiyar shugabar mata Umoru Hadizat; Mataimakiyar babban mai binciken kudi Devine Amina Arong; Mataimakin sakataren tsare-tsare Hassan Yakubu; da mataimakin sakataren kudi na kasa Irona Alphonsus.

Wannan lamari dai ya zo a ba zata, duk da yake an dade ana cece-kuce akan shugabancin jam’iyyar a karkashin Uche secondus.

To sai dai kungiyar gwamnonin PDP ta yi kira ga bangarorin da ke takaddama da juna da su mayar da wukakensu kube, domin ceto jam’iyyar ta adawa daga tarwatsewa.

“PDP ce kawai fatan da ya rage wa ‘yan Najeriya, don haka ya kamata ta nuna misali ga ‘yan kasar, ta kuma yi kyakkyawan amfani da matsalolin da suka dabaibaye APC” in ji sanarwar ta Aminu Tambuwal.

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

Sanarwar ta ba da tabbacin cewa ana nan ana kokarin shawo kan wannan takaddama cikin ruwan sanyi, tare da bin dukan tanade-tanaden kundin tsarin mulki na kasa da na jam’iyyar, domin tabbatar da yi wa kowa adalci.

To amma kuma ko baya ga shugabannin 7 da suka yi murabus, shi ma shugaban matasa na kasa na jam’iyyar Sunday Ude-Okoye, ya yi kira ga shugaban jam’iyyar Uche Secondus da yayi murabus daga mukaminsa, saboda abin da ya kira “kasawa wajen tafiyar da lamurran jam’iyyar kamar yadda ya kamata.”

Ude-Okoye fa fadawa manema labarai jim kadan bayan murabus na shugabannin 7, cewa “Secondus ya tarwatsa bangarori daba-daban na jam’iyyar, haka kuma ya haifar da babbar baraka a shugabancinta.”

Shugaban Jam'iyyar PDP, Uche Secondus
Shugaban Jam'iyyar PDP, Uche Secondus

Ya ci gaba da cewa ko bayan shi, da shugabannin 7 da suka yi murabus, akwai wasu da dama da suke da dimbin korafe-korafe a shugabancin jam’iyyar, wanda kuma idan ba’a dauki matakin janye Secondus ba, jam’iyyar za ta iya rasa su baki daya.

To sai dai da yake maida martani akan wadannan zarge-zargen, mai baiwa Uche Secondus shawara kan kafafen sada zumunta na zamani. Ike Abonyi, ya ce soki burutsu ne kawai na ‘yan siyasa, yana mamakin yadda shugaban matasan zai fito ya zargi Secondus da kasawa a yanzu, bayan yayi aiki tare da shi tsawon tsawon shekaru a can baya.

XS
SM
MD
LG