Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zuwan Buhari London Barnar Kudi Ne, Saboda Taron Ta Yanar Gizo Ake Yi – PDP


Taron da gwamnonin jam'iyyar PDP suka yi a Bauchi (Facebook/PDP)

Fadar shugaban kasar ta sha bayyana cewa Buhari kan je kasar waje don duba lafiyarsa tun ma kafin ya zama shugaban kasa.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce balaguron da shugaban kasar ya yi zuwa London don ya halarci taron bunkasa fannin sha’anin ilimi na duniya da Burtaniya ke karbar bakuncinsa, ba wani abu ba ne illa barnar dukiyar kasa.

Cikin wata sanarwa da ta fitar da yammacin ranar Talata dauke da sa hannun sakataren yada labaranta na kasa Kola Ologbondiyan, PDP ta ce taron za a gudanar da shi ne ta yanar gizo.

“Abin takaici ne a ce Shugaba Muhammadu Buhari ya dauki dukiyar kasa ya yi tafiya zuwa London don halartar taron koli na bunkasa ilimi a duniya, alhali taron an tsara za a gudanar da shi ne ta kafar yanar gizo.”

Jam’iyyar ta kuma caccaki fadar shugaban kasar kan yadda ta fake da taron wanda za a yi ta yanar gizo don ya je ya ga likitocinsa.

“Wannan har ila yau wata dabara ce ta boye gazarwarsa wajen kasa cika alkawarin da ya yi a lokacin yakin neman zabe a 2015, inda ya ce ba zai sake zuwa ganin likita a kasar waje ba idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Lokacin da shugaba Buhari ya isa London don halartar Taron bunkasa sha'anin ilimi na duniya (Facebook/ Femi Adesina)
Lokacin da shugaba Buhari ya isa London don halartar Taron bunkasa sha'anin ilimi na duniya (Facebook/ Femi Adesina)

“Abin takaici ne a ce shugaban kasa yana can yana kashe kudaden masu biyan haraji yana samun kulawar kwararrun likitoci a London yayin da miliyoyin ‘yan Najeriya na can suna mutuwa a asibitoci marasa kyau a gida.”

A ranar Litinin fadar shugaban kasar ta sanar da cewa Buhari zai je taron bunkasa sha’anin ilimi na duniya a London inda daga nan zai tsaya na wasu ‘yan kwanaki don ya ga likitocinsa.

Fadar shugaban kasar ta sha bayyana cewa Buhari kan je kasar wajen don duba lafiyarsa tun ma kafin ya zama shugaban kasa.

A mako na biyu cikin watan Agusta me kamawa ake sa ran shugaban zai koma Najeriya a cewar sanarwar da Kakakinsa Femi Adesina ya fitar a ranar Litinin.

A dai farkon makon nan ne jam’iyya mai mulki ta APC ta ja hankalin babbar jam’iyyar adawar bayan taron da PDP ta yi a Bauchi, kan ta mayar da hankali wajen magance matsalolin cikin gida da ke damun ta maimakon dora laifi akan APC.

Gwamnonin PDP a wani taro da suka yi kwanan nan (Twitter/ PDP)
Gwamnonin PDP a wani taro da suka yi kwanan nan (Twitter/ PDP)

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin, babban sakataren jam’iyyar APC karkakashin kwamitin rikon kwarya, Sanata John Akpanudoedehe ya ce, al’amuran da PDP ta bijiro da su babu kamshin gaskiya a cikinsu.

“An ja hankalinmu kan wata sanarwa da kungiyar gwamnonin PDP ta fitar, wacce ke kunshe da karerayi da makirce-makirce kan halin da kasa ke ciki.

“Kamata ya yi PDP ta hanzarta magance matsalolinta, lura da yadda mambobinta da shugabanninta ke komawa APC saboda kwadaituwa da suka yi da tsarin mulkin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.” Kpanudoedehe ya ce.

XS
SM
MD
LG