Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Takaddama Ta Kaure Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Rev. Matthew Kukah


Malam Garba Shehu, Kakakin shugaban Najeriya (Instagram/ Garba Shehu)
Malam Garba Shehu, Kakakin shugaban Najeriya (Instagram/ Garba Shehu)

Wannan dai ba shi ne karon farko da fadar shugaban kasar da fitaccen malamin addinin suke kai ruwa rana ba, ko a watan Afrilu, sun yi ka-ce-na-ce bayan da Bishop Kukah ya yi tsokaci kan yadda matsalar tsaro take kara ta’azzara a Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta nuna takaicinta bisa kalaman da ta ce babban malamin addinin Kirista Bishop Matthew Kukah ya yi a gaban majalisar dokokin Amurka kan kasarsa Najeriya.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, kakakin shugaba Shugaba Muhammadu Buhari Malam Garba Shehu ya shawarci malamin addinin Kiristan da ya guji furta kalaman da ka iya haddasa husuma a tsakanin al’uma.

A farkon makon nan Bishop Matthew Kukah ya bayyana gaban majalisar dokokin Amurka ta yanar gizo inda rahotanni suka ce ya ce ana muzgunwa mabiya addinin Kirista a Najeriya karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Sai dai fadar shugaban kasar ta ce, wadannan kalamai da Bishop Kukah ya bayyana “ra’ayi ne na gashin kansa, ba na jama’ar da suka fi rin jaye ba ne.”

“Ya kamata shugabannin addini da ke wa’azi kan gaskiya, su san cewa akwai hakki da ya rataya a wuyansu su ga cewa suna aikata abin da suke wa’azi akai.” In ji Garba Shehu.

Karin bayani akan: Kiristoci, Musulmai, Muryar Amurka, Bishop Matthew Kukah, jihar Kebbi, jihar Katsina, Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, Nigeria, da Najeriya.

Gwamnatin ta Najeriya har ila yau ta nuna damuwa kan yadda malamin addinin ya ware wata kabila guda yana sukar ta, tana mai cewa ikirarin da ya yi cewa an fi kaikaitar makarantun Kiristoci idan za a yi satar dalibai zance ne da ba shi da tushe balle makama.

“Tare da nuna girmama matsayar da malamin addinin ya dauka, bayanan da suke a bayyane karara, sun nuna cewa ikirarin da ya yi cewa ‘yan bindiga ko ‘yan ta’adda na kaikaitar makarantun Kiristoci ba daidai ba ne.”

“Abin takaici ne, amma da gaske ne ‘yan bindiga Musulmai sun sace daliban Kankara a jihar Katsina wadanda Musulmai ne. Hakazalika, ana rike yanzu haka da daliban Islamiyya 134 daga Tegina a jihar Neja. Haka kuma al’umar kasar nan sun shaida yadda aka sace daliban Jengebe a jihar Zamfara da kuma dalibai sama da 100 a Yauri da ke jihar Kebbi.”

Yunkurin da Muryar Amurka ta yi don jin ta bakin fitaccen malamin addinin ya ci tura, domin bai amsa sakon tes da aka aika masa ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Wannan dai ba shi ne karon farko da fadar shugaban kasar da fitaccen malamin addinin suke kai ruwa rana ba, ko a watan Afrilu, sun yi musayar kalamai bayan da Bishop Matthew Kukah ya yi tsokaci kan yadda matsalar tsaro take kara ta’azzara a Najeriya.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG