Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Martanin Da Fadar Shugaban Najeriya Ta Mayarwa Matthew Kukah


Mai magana da yawun Shugaban Kasa kuma mai bai wa shugaba Buhari shawara kan sha’annin yada labarai, Garba Shehu, ya fitar da wata sanarwa a Abuja da ta zargi Rev. Kukah da saka siyasa da ta bakanta Shugaba Muhammadu.

Yayin da yake mayar da martani ga sakon Kukah, inda malamin ya ce rikicin Boko Haram ya ta’azzara a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari, Shehu ya bayyana sukar da Bishop Matthew Hassan Kukah ke yi wa gwamnatin Buhari, a matsayin na marasa tsoron Allah.

Ya ce “Duk ‘yan kasa suna da akidojinsu na daban, hatta nau’ukansu na gaskiya. Amma idan ka ce kai bawan Allah ne, kamar yadda Rev. Mathew Hassan Kukah yake yi, akida bai kamata ta tsaya ga hanyar gaskiya da adalci ba. ”

“Rev. Kukah ya faɗi wasu abubuwa waɗanda ba za a iya fassarawa ba a yayin wa’azin da ya yi na Ista. Amma, da yake cewa ta'addancin Boko Haram ya fi wanda aka yi a 2015 muni, bai yi magana kamar bawan Allah ba. Kukah ya kamata ya je Borno ko Adamawa don tambayar al’ummar bambanci tsakanin 2014 da 2021.

“Hakazalika, batun Hijabi a Jihar Kwara, magana ce ta jiha wacce kotunan kasar suka yanke hukunci a kanta. Batutuwa ne da suka bayyana a jihohi da dama tun lokacin gwamnatin Obasanjo. A duk wannan, yaushe kuma sunan Shugaba Buhari ya bullo cikin al’amarin?

“Yana taka rawar siyasar bangaranci inda ya ke jan Shugaban kasa cikin lamarin. Gwamnatin da ta kirkiro wata ma’aikata na kanta, a karon farko a tarihin kasar, don magance matsalolin ‘yan gudun hijirar, ya za a yi a zarge ta da gazawar kula da su.

XS
SM
MD
LG