Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sadio Mane Ya Kamu Da COVID-19


Dan Wasan Liverpool Sadio Mane.

Dan wasan kungiyar Liverpool ta Ingila Sadio Mane, yana zaman killacewa, bayan an auna shi yana dauke da cutar coronavirus.

Lamarin na zuwa ne kwanaki 3 bayan da kungiyar ta ba da sanarwar cewa wani dan wasanta Thiago Alcantara ya kamu da cutar.

Dan Wasan Liverpool Thiago Alcantara
Dan Wasan Liverpool Thiago Alcantara

Kungiyar ta Liverpool ta ce Mane ya nuna kananan alamomin cutar ne, to amma yana cikin koshin lafiya da kuzari.

Mane, dan kasar Senegal mai shekaru 28, ya bugawa kungiyar ta shi wasan da ta buga da Arsenal a ranar Litinin, to amma bai buga wasan da ta kuma bugawa da kungiyar ba a ranar Alhamis da ta gabata.

Kungiyar ta fitar da sanarwar cewa tana ci gaba da ba da kulawa sosai ga ‘yan wasan nata da ke dauke da cutar, kamar yadda sharuda da dokokin cutar ta COVID-19 suka tanada.

A ranar Litinin kuma hukumar shirya gasar Premier ta Ingila ta ba da sanarwar cewa an sami mutane 10 sun kamu da cutar ta coronavirus a gwajin da aka yi na baya-bayan nan, adadi mafi yawa tun somawar kakar wasanni ta bana.

Facebook Forum

Diego Maradona 1960-2020
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:07 0:00
Karin bayani akan Diego Maradona
XS
SM
MD
LG