Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Yace Sai Ya Sake Duba Kasafin Kudin Bana Kafin Ya Saka Hannu


Shugaba Buhari da Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry

Shugaba Muhammadu Buhari, yace tabbas zai duba kasafin kudin bana da majalisar dokokin Najeriya ta amince kafin ya rattaba hannu ta fara aiki.

Buhari yayi wannan furuci ne alokacin wani taro da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, Shugaba Buhari yace saboda wasu abubuwa da aka cunkusa cikin kasafin kudin, dole sai ya gani da idanunsa da tabbatarwa kafin ya sa hannu.

Shugaban yace “wasu jami’an gwamnati sun fitar da wasu abubuwa da muka saka ciki sannan suka cunkusa abubuwan da suke so. Dole ne na kalli kasafin da yan majalisu suka fitar da idanuna, na duba ma’aikatu bayan ma’aikatu, domin tabbatar da cewa kasafin shine wanda muka rubuta.”

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa zata ci gaba da yaki da hukunta duk wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa, shugaban kuma ya sami karfin gwiwa daga sakatare Kerry na cewa gwamnatin Amurka zata taimakawa Najeriya wajen sake dawowa da duk kudin da aka sace wanda ke cikin bankunan Amurka.

Sakatare Kerry ya yabawa gwamnatin shugaba Buhari, kan nasarar da take samu wajen yaki da kungiyar Boko Haram, yana mai cewa Amurka zata ci gaba da baiwa Najeriya duk taimakon da take bukata don tabbatar da ganin an kawo karshen duk wata kungiyar dake kawo barazana ga tsaron kasa.

XS
SM
MD
LG