Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Sanar Da Karin Tallafi Na Kusan Dala Milliyan 150 Ga Nijar Da Wasu Kasashen Yankin Sahel

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Suna Gaisawa Da Shugaban Nijar Mohamed Bazoum A Fadar Shugaban Kasa A Niamey, Niger, Maris 16, 2023.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Suna Gaisawa Da Shugaban Nijar Mohamed Bazoum A Fadar Shugaban Kasa A Niamey, Niger, Maris 16, 2023.

Sakataren harakokin wajen Amurka Antony Blinken da ke ziyarar wuni biyu a jamhuriyar Nijar ya sanar da karin kudaden tallafi ga kasashen yammaci da tsakiyar Afrika wadanda za'a yi amfani da su don inganta rayuwar al’umomin wadannan kasashe.

NIAMEY, NIGER - Amurka da Nijar da ke Allah wadai da mamayar Russia akan Ukraine, sun jaddada anniyar ceto dimokradiya a kasashen yankin Sahel da suka fada karkashin mulkin soja, domin hanya ce da ke da tasirin gaske wajen murkushe matsalolin ta’addanci da na kuncin rayuwar da ake fama da su.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Ya Sanar Da Karin Tallafi Na Kusan Dala Million 150 Wa Nijar
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Ya Sanar Da Karin Tallafi Na Kusan Dala Million 150 Wa Nijar

A taron manema labarai da suka kira da yammacin ranar Alhamis da takwaransa na Nijar, Hassoumi Massaoudou, bayan ganawa da shugaba Mohamed Bazoum sakataren harakokin wajen Amurka Antony Blinken ya ba da sanarwar karin dalar Amurka million kusan 150 domin ayyukan jin ‘kai a Afrika ta yamma, ta tsakiya da Sahel.

Blinken ya ce wannan tallafi zai shafi kiwon lafiya, samar da abinci ruwan sha, tsafta da bukatun ‘yan gudun hijira.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Ya Sanar Da Karin Tallafi Na Kusan Dala Million 150 Wa Nijar
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Ya Sanar Da Karin Tallafi Na Kusan Dala Million 150 Wa Nijar

Matsalar tsaro a yankin Sahel da koma bayan da aka fuskanta a kasashen Mali da Burkina Faso inda soja suka kifar da gwamnatocin fararen hula na daga cikin matsalolin da Amurka da Nijar suka jaddada aniyar magancewa.

Hassoumi Massaoudou ministan harakokin wajen Nijar, ya ce "wajibi ne a fara magance matsalar shugabanci da rarrabuwar kawuna tsakanin al’umma da aka gaza warwarewa a wasu wurare inda ‘yan ta’adda ke amfani da irin wannan rauni. Saboda haka mu ke da tsarin samar da sulhu a tsakanin jama’a domin kaucewa barkewar tashin hankali tsakanin wannan al’umma da waccan."

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Ya Sanar Da Karin Tallafi Na Kusan Dala Million 150 Wa Nijar
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Ya Sanar Da Karin Tallafi Na Kusan Dala Million 150 Wa Nijar

Ya ci gaba da cewa "Wannan wani bangare ne na yakin da muka sa gaba. Haka kuma ya na da kyau a maida hankali akan ayyukan ci gaba a daidai lokacin da ake gwabza yaki."

"To haka muke yi don kashe wuta a yankunan dake fama da rikici. Ku dubi kasashen da suka dogara da Wagner a fili za'a gane cewa dukkansu suna fama da raunin shugabanci."

Antony Blinken ya gana da wasu matasan da suka tuba daga ta’addanci da nufin tantance zahirin matsalolin da ke tura matasa cikin wannan aika aika.

A karshe kuma ya yi alkawarin bayar da gudunmowar kudaden da za'a yi amfani da su don koyar da su sana’oi.

US Secretary of State Antony Blinken, left, meets with Nigerien Foreign Minister Hassoumi Massoudou at the Diori Hamani International Airport in Niamey, Niger, on March 16, 2023.
US Secretary of State Antony Blinken, left, meets with Nigerien Foreign Minister Hassoumi Massoudou at the Diori Hamani International Airport in Niamey, Niger, on March 16, 2023.

Katafaren shirin nan na hadin guiwar Nijar da Benin wanda Amurka ke daukar dawainiyarsa wato "Programme Regional Millemium Challenge Corporation" na daga cikin abubuwan da Blinken ya tattauna a kansu da hukumomin Nijar.

Amurka da Nijar wadanda tun tashin farko suka yi tir da mamayar Russia a Ukraine, sun kara jaddada cewa suna nan kan bakansu domin abubuwan da ke faruwa a wannan yaki babban laifi ne na tauye hakin ‘dan adam da kuma fatali da dokokin kasa-da-kasa.

Saurari cikakken rahoto daga Soule Moumouni Barma:

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Ya Sanar Da Karin Tallafi Na Kusan Dala Million 150 Wa Nijar.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

XS
SM
MD
LG