Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Zai Kai Ziyara Najeriya


Wata tattaunawa ta yanar gizo da Blinken ya yi da Buhari a baya
Wata tattaunawa ta yanar gizo da Blinken ya yi da Buhari a baya

Ana sa ran Blinken zai gabatar da wani jawabi kan dagantakar Amurka da nahiyar Afirka sannan zai gana da ‘yan kasuwa a fannin fasahar zamani ta yanar gizo a birnin na Abuja.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken na shirin kai ziyara nahiyar Afirka a tsakanin ranakun 15 zuwa 20 ga watan Nuwamba.

Wata sanarwa da shafin yanar gizon ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta wallafa, ta ce Blinken zai kai ziyara ne a kasashen Kenya, Najeriya da Senegal, a wani yunkurin na kara kyautata dangantakar Amurka da kasashen da ma nahiyar baki daya.

Daga cikin batutuwan da ziyarar za ta fi mayar hankali akai akwai batun matsalar annobar COVID-19, farfado da tattalin arzikin duniya, yaki da matsalar sauyin yanayi, dabbaka tsarin dimokradiyya da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Sakatare Blinken a cewar sanarwar zai fara yada zango ne a Nairobi, babban birnin Kenya, inda zai gana da shugaba Uhuru Kenyatta da Sakatariyar gwamnati kan harkokin waje Ambasada Raychelle Omamo.

Daga nan kuma zai dangana da Abuja, babban birnin Najeriya, inda zai gana da shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osibanjo da kuma ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama inda za su tattauna kan tsaro a duniya, bunkasa tattalin arziki da jaddada tsarin mulkin dimokradiyya

Ana sa ran Blinken zai gabatar da wani jawabi kan dagantakar Amurka da nahiyar Afirka sannan zai gana da ‘yan kasuwa a fannin fasahar zamani ta yanar gizo a birnin na Abuja.

Daga Abuja kuma Blinken zai karasa zuwa Dakar babban birnin Senegal inda a nan ma zai gana da shugaba Macky Sall da ministar harkokin waje Aissata Tall Sall don karfafa zumuncin Amurka da Senegal

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG