Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry Yana Kasar Habasha


John Kerry a Afrika

Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya doshi kasar Habasha don tattaunawa kan batutuwan tsaro da shugabannin yankin, da kuma halartar bukin zagayowar ranar kafa kungiyar Tarayyar Afirka karo na 50.

Daga yau Jumma’a Kerry zai fara ziyarar ta sa ta tsawon kwanaki biyu a birnin Addis Ababa, inda a cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, zai gana da manyan jami’an gwamnatin kasar Habasha don tattaunawa kan batutuwan da su ka shafi kasashen biyu.

Gobe Asabar zai bi sahun shugabannin kasashen Afirka da sauran manyan baki daga wasu kasashen a babban taron kungiyar Tarayyar Afirka, inda za'a yi bikin cika shekaru 50 da kafa kungiyar Tarayyar Afirka din, wadda a baya ake kiranta Kungiyar Hadin Kan Afirka (OAU).

Ana kyautata zaton ziyarar ta Kerry za ta hada da tattaunawa kan fafatukar da ake yi da masu tsattsauran ra’ayin Islama a kasashe irin su Mali da kuma arewacin Nijeriya.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG