Accessibility links

Sallah Ta Kayatar A Tahoua, Jamhuriyar Nijar


Irin taron da aka saba yi na sallar Eid a kasashen Musulmi. Wannan a dandalin Ramat na Maiduguri, lokacin sallar azumi.

Gwamnan Jihar Tahoua, Barmo Salihou, yayi kira ga 'yan jihar da su yawaita addu'o'i domin kaucewa matsaloli na tashin hankali.

A Jamhuriyar Nijar, an gudanar da bukukuwan Sallar layya, Eid el-Kabir, cikin lumana da kwanciyar hankali kamar yadda aka yi a sauran sassa na duniya.

Wakilin VOA Hausa da ya halarci sallar Eid da bukukuwan da suka biyo baya a birnin Tahoua, Abdoulaye Mamane Ahmadou, yace dubban Musulmi sun fito cikin yanayi na murna da annashuwa domin wannan bukin.

Gwamnan Jihar Tahoua, Barmo Salihou, yayi jawabi ga al'ummar jihar inda yake rokon duk Musulmi da su rungumi yin addu'o'i da saukar Qur'ani domin neman kaucewa matsaloli masu nasaba da tashin hankali a cikin jihar ta su. Yana wannan rokon ne a yayin da ake fama da fitinar siyasa a kasar ta Nijar.

Gwamna Salihou yace yana da kyau a kasance cikin addu'a kowane lokaci saboda a koyaushe ana bukatar ganin kasa ta samu kwanciyar hankali.

Amma a wani abinda sai a Jihar Tahoua kawai ake yi lokacin Sallah, mahukunta sukan dauki magana zuwa ga jama'a kai tsaye, su na neman gafarar jama'a tare da gafartawa wadanda suka yi musu wani laifin.

Haka mai Martaba Sarkin Tahoua, Alhaji Abdou, yayi yau da safe, inda yake cewa, "Ni abinda ke tsakani na da 'yan'uwa duk, na yafe musu, ko wanene. Ku ma ina neman yafewa (daga) gareku."

Sannan Sarkin na Tahoua yayi addu'ar Allah Ya bayarda zaman lafiya da albarka a cikin kasa.

Wakilin namu dai ya zagaya cikin tahoua inda ya tarar da jama'a cikin murna da farin ciki su na gudanar da hidimomin Sallar.

XS
SM
MD
LG