Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama Da Kashi 40 Cikin 100 Na Fama Da Rashin Aiki A Najeriya


Al'ummar Najeriya

Yawan marasa aikin yi a Najeriya ya karu zuwa kusan kashi talatin cikin dari a wannan shekarar inda ya kai miliyan 16, a cewar rahotan da hukumar kididdiga ta fitar na watan Nuwamba.

Haka kuma ana ra san karin wasu mutane miliyan biyu zasu rasa aikinsu a karshen wannnan shekarar. Wannan mummunan labari na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ta wuce kasar Indiya inda ta zamanto kasar ta fi yawan mutanen dake fama da talauci a duniya, gabannin zaben shugaban kasar da ke tafe a watan Fabarairu.

A watan Satumbar shekarar da ta gabata Najeriya ta fita daga cikin matsalar tattalin arziki mafi muni da ta taba fuskanta cikin shekaru talatin, inda yanzu ake fatan ta samu farfadowa.

Amma rashin aikin yi da talauci na ci gaba da samun gindin zama a kasar da kashi arba'in cikin dari na al'ummar kasar miliyan dari biyu ke fama da rashin aiki kwata-kwata.

Najeriya na bukatar ta kirkiro ayyukan yi Miliyan hudu a duk shekara, idan har ana son fita daga cikin wannan kangi, wanda ke zama babban kalubale ga duk wanda ya sami nasarar lashe zaben na watan Fabarairu.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG