Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Sama Da 700 Sun Kubuta Daga Hannun Boko Haram


Wasu Daga Cikin Mutanen Da Sojojike Kula da su

Rundunar sojan Najeriya tace sama da mutane 700 da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa dasu sun arce daga inda ake tsare da su a yankin arewa maso gabashin kasar.

Mai Magana da yawun rundunar sojan Najeriya Col. Timothy Antigha yace yanzu haka am baiwa wadanda suka arcen matsuguni a sansanin sojoji dake garin Monguno na jihar Borno.

Sai dai kuma Antigha bai bayyana lokacin da wadannan mutane suka gudo ba da kuma ko har yanzu suna karkashin kulawar soja. Har zuwa yanzu babu wata kafar da ta tabattarda sahihancin ikirarin sojojin.

A sanarwar da ya bada, Col. Antigha yace wadanda aka yi garkuwa dasu sun hada da maza da mata da yara kuma yan taddan sun tilasta musu yin ayyukan gona a tsibirai da dama dake yankin tabkin Chadi.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG