Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Sanatoci Sun Ce Ba Su Goyi Bayan Sauya Tsarin Zaben Da Majalisar Dattijai Ta Yi ba


Wasu sanatocin Najeriya dake bayyana rashin amincewarsu da sauya tsarin zabe

Kan majalisar dattijan Najeriya ya rabu gida biyu a bayan da shugaban majalisar, Bukola Saraki, ya tabbatar da rahoton amincewa da sauya jadawalin zaben 2019 wanda ya saba da wanda hukumar zabe ta gabatar

'Yan majalisar dattijan Najeriya da dama sun fito su na bayyana adawarsu da matakin da shugaban majalisarsu, Bukola Saraki, ya dauka na ayyana amincewa da rahoton sauya jadawalin gudanar da zaben shekarar 2019, wanda ya saba da tsarin da hukumar zaben kasar ta gabatar na gudanar da wannan zabe.

A lokacin da suke jawabi ga 'yan jarida a Abuja, Sanata Ovie Omo-Agege, daga Jihar Delta, yace shugabannin majalisar sun take tsarin gudanar da aikin majalisa ta hanyar hana su damar nuna adawarsu ga wannan matakin.

A dalilin haka ne su wadannan 'yan majalisa suka shura takalmansu suka fice daga cikin zauren majalisa.

Wakiliyar Muryar Amurka, Medina Dauda, ta ce kawunan sanatocin sun rabu gida biyu tun daga lokacin da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya tabbatar da amincewa da rahoton sauya jadawalin zaben 2019, wanda ya sha bambam da tsarin da ita hukumar zaben Najeriya INEC ta gabatar. Saraki da wanda suka goyi bayan wannan abu, su na son da a fara gudanar da zaben shugaban kasa tukuna.

Sanata Abdullahi Adamu, wanda ya jagoranci masu adawa da gyara dokar zaben, ya fadawa wakiliyarmu cewa a fili yake cewa tsarin mulkin Najeriya ya bayyana a fili ko wanene yake da ikon saka ranar zabe, ko tsarin gudanar da zabe.

Yace Hukumar zabe ta kasa, INEC, ita ce tsarin mulkin Najeriya ya ba wannan ikon.

Sanata Abdullahi Adamu yace an sa majalisa a yanzu ta yi wata doka wadda ta saba da kundin tsarin mulkin kasa.

Sai dai a lokacin da yake kare wannan mataki da aka dauka na yin gyara ga dokar, mai magana da yawun majalisar dattijai, Aliyu S. Abdullahi, yace wannan mataki bai saba da tsarin mulki ba, domin a shekarar 2010 an yi gyara ga tsarin mulki inda aka ce hukumar zabe zata sa ranakun zabe aka kara da cewa "kamar yadda dokar zabe ta tanada."

Yace abinda aka yi a yanzu, shine an yi gyara ne ga wannan doka ta zabe.

Medina Dauda ta ce babu tabbas ko shugaba Muhammadu Buhari zai yarda ya sanya hannu a kan wannan dokar zabe ta 2018 da majalisar dattijan ta yi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG