Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Sake Jaddada Umurninsa Ga Sojojin Najeriya, Cewa Su Ragargaji Miyagu


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:03 0:00

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Yau Alhamis shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nanata cewa shugabannin hukumomin tsaro sun samu umurninsa cewa su dau tsauraran matakai kan miyagu, da kuma duk wanda aka kama da bindigar AK-47 ba bisa ka'ida ba.

Shugaban ya yi wadannan kalaman ne a wani taron da ya yi da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Najeriya a gidan gwamnati, wanda ya samu jagorancin hadin gwiwar Sarkin Musulmi na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku da babban sarkin kasar Yarbawa Ooni of Ife, Adeyeye Enitan Ogunwusi.

Taron ya samu halartan shugabannin hukumomin tsaro da suka hada da mai bada shawara a kan tsaron kasa, Major-General Babagana Monguno da Sifeto janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu Abubakar da babban darektan Ma’aikatar Kula da Harkokin Kasa, Yusuf Bichi da kuma Babban Darektan Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Kasa, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.

Karin bayani akan: Shugaba Muhammadu Buhari​, Ahmed Rufai Abubakar, Nigeria, da Najeriya.

Shugaban kasa ya fada wa taron kokarin da gwamnati ke yi wurin daukar matakan kyautata tsaro a cikin kasar, yana mai cewa gwamnatinsa ta samu nasarori da dama a arewa maso gabas da kuma kudu maso kudancin kasar.

Ya ce “Amma wani abin al’ajabi da ke faruwa a yanzu a arewa maso yamma, mai al’umma iri guda da kuma al’adu iri guda, shi ne suna kashe juna, suna kwashe dabbobinsu kana suna kona dukiyoyinsu.

“A dalilin haka ne muka yi wata ganawa ta sa’o’i hudu da majalisar tsaro ta kasa da ta samu halartar ministocin Harkokin Cikin Gida da na tsaro da na Harkokin Waje da Babban Hafsan Soji da shugabannin sojoji da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da wasu da dama, kana muka ba su umarni dalla dalla.

“Wani batu guda da ya isa ga kafafen labarai, wanda ni kaina na karanta, shi ne duk wanda aka samu da bindigar AK-47 a harbe shi."

Shugaban kasar ya nuna takaicinsa a kan hare hare da miyagu ke kaiwa tashoshin ‘yan sanda suna kashe jami’an tsaro, inda ya yi kashedi cewa babu wani mai zuba jari da zai kai dukiyarsa a kasar da bata da tsaro.

Shugaba Muhammadu Buhari​ ya kuma nanata muhimmancin sarakunan gargajiya wajen amfani da mukamai da ayyukansu wurin hada al’ummomi da kokarin da gwamnati ke yi na tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Da yake kara maimaita umurninsa ga sababbin shugabannin sojojin kasar game da inganta yanayin tsaro, Shugaban Kasa ya ce samun cimma nasarar inganta tsaro zai zo ne ta hanya daya tilo: ta yin aiki tare, da kuma hadin gwiwa da sarakunan gargajiya da sauran hukumomi, da suke taka muhimmiyar rawa a zamantakewar al’umma.

XS
SM
MD
LG