Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Kano Ya Bukaci hadin Kai Tsakanin Al'umomin Jihar Kano


Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Alkibilar hudubar Limaman masallatan Idi a birnin Kano da kewaye ta zo wuri guda ta fuskar jan hankalin jama’a, shugabanni da mabiya wajen kaucewa duk wani al’amari da zai haifar da fitina a tsakanin al’uma.

Miliyoyin al’umar musulmi ne suka gudanar da Sallah a masallatan idi daban daban kimani dari dake sassan birnin Kano, da kewaye.

Dr. Muhammadu Sani Ayagi, wanda ya jagoranci Sallar Eid Fitr, a masallaci harabar tsohuwar jami’ar Bayero dake Kano, baya ga tambihi akan bukatar al’umar Musulmi suyi riko da darussan da suka koya a Ramadan, Malamin ya hori ‘yan siyasa dasu yi la’akari da maslahar al’uma a yayinda da suke fafutukar cimma muradunsu na kama madafun iko.

Ya kara da cewa al’umar Musulmi siyasa ta dade tana yiwa al’umar Musulmi illa saboda haka yace ya zama wajibi a dauke son zuciya domin daukar abinda Allah yake so.

A jawabansu na Sallah Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu, sun nanata mahimmancin hadin kai tsakanin al’umomi daban daban da suke zaune a jihar Kano.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG