Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Qatar Ya Kauce wa Batun Iran a Ganarwarsa Da Trump


Sarkin Qatar ya yi amfani da ziyarar da ya kawo a nan birnin Washington DC a wannan mako inda ya bayyana irin kyakkyawar dangantakar tattalin arziki da ta tsaro da ke tsakanin Amurka da kasarsa, amma bai ce komai ba dangane da yunkurin da yake yi na shiga tsakanin takaddamar Amurka da Iran ba.

Sheikh Tamim Bin Hamad Al Thani, ya gana da shugaba Donald Trump a fadar White House a jiya Talata da kuma mukaddashin sakataren tsaro Mark Esper a ma’aikatar tsaro ta Pentagon, inda dukkan bangarorin biyu suka yabawa kyakkyawar dangantaka ta musamman ta tsaro da ke tsakninsu.

Sun kuma bayyana kokarin da kasar ta Qatar ke yi na sayen jirgin yaki kirar Amurka da da sauran makamai, kana da yabawa kasar wajen fadada filin jirgin ta na Al Udeid wanda jiragen yakin Amurka ke sauka.

Sai dai bayanan da Amurka ta fitar kan haduwa da Al Thani ya yi da Shugaba Trump da Esper, ba su fito karara sun yi magana kan takaddamar da aka kwashe watannin ana yi tsakanin Amurka d Iran ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG