Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Gargadi Kasar Iran


Shugaban Amurka Donald Trump ya yiwa Iran kashedi “tayi hankali” bayan ta fada a jiya Lahadi cewa zata kara inganta sinadarin uranium dinta fiye da abin da aka kayyade mata a cikin yarjejeniyar nukiliya a shekarar 2015

Trump ya yi wadannan kalaman ne bayan da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya fitar da wani sakon twitter cewa shawarar da Iran ta dauka zai kara mai da ita saniyar ware kuma a kara mata takunkumai.

Yakamata kasashe su ci gaba da riko da yarjejeniyar da aka cimma a baya cewa Iran ba zata inganta shirinta na makaman nukiliya. Idan gwamnatin Iran ta mallaki nukiliya zata zama babban hadari ga duniya a cewar sakon twitter Pompeo.

Birtaniya tayi kira ga Iran ta dakatar da ayyukanta nan da nan kuma ta wargaza shirinta kana tayi riko da abubuwa dake kunshe a cikin yarjejeniyar da ita kanta ta amince da iyaka da aka mata a shirinta na nukiliya kana itama ta amfana da dage takunkuman tattalin arziki a kanta.

Faransa tace mataki da Iran ta dauka ya sabawa yerjejeniyar kasa da kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG