Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Sudan Na Kontagora Alhaji Sa'idu Namaska Ya Rasu


Sarkin Sudan Na Kontagora, Alhaji Sa'idu Namaska.
Sarkin Sudan Na Kontagora, Alhaji Sa'idu Namaska.

Gwamnatin jihar Naija da ke Arewa maso yammacin Najeriya ta ba da sanarwar rasuwar Mai Martaba Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Sa'idu Namaska.

Wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin jihar ta Naija Ahmed Ibrahim Matane ya fitar, ta ce sarkin ya rasu ne a asibitin Nizamiye da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, bayan fama da rashin lafiya.

Matane ya ce Gwamnatin Jihar Naija da masarautar Kontagora na cikin wani yanayi na alhini da kaduwa akan wannan babban rashi.

Shi ma kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Naija, Barista Abdulmalik Sarkin Daji, wanda basarake ne a masarautar Kontagora, ya ce Arewacin Najeriya baki daya sun yi rashin jigo, bisa la'akari da gudummuwar da ya bayar wajen hadin kan yankin.

Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Sa'idu Namaska, wanda jika ne ga Ummaru Nagwatse, jinin Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo, ya rasu yana da shekaru 84 a duniya, ya kuma share tsawon shekaru 47 akan karagar mulkin masarautar Kontagora.

Sanarwar ta ce za'a gudanar da jana'izarsa da misalin karfe 4 na yammacin yau Alhamis, a fadarsa da ke Kontagora.

XS
SM
MD
LG