Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudiya Ta Tsagaita Hare-hare Akan Yemen


Motoci da hare-haren Saudiya suka rugurguza a Yemen
Motoci da hare-haren Saudiya suka rugurguza a Yemen

Saudiya ta nasarda kawo karshen hare-haren da ita da wasu kasashen da take yiwa jagoranci suke kaiwa kan 'yan tawayen Houthi a Yemen.

Kasar Saudi Arabiya ta ce ta tsai da hare-haren jiragen saman hadin gwiwar kasashen Larabawa, wanda ta ke jagorantar kaiwa kan 'yan Houthi a Yemen, to amma ba za ta daina matsa ma 'yan tawayen lamba ba.

Wasu jami'an gwamnatin Saudiyyar sun fada jiya Talata cewa bayan ruwan bama-baman da aka shafe makonni hudu ana yi, 'yan Houthin sun rasa karfin yin barazana ga farar hulan Yemen ko kuma wasu kasashe, ciki har da kasar ta Saudiyya.

Su ka ce yanzu za’a shiga wani sabon babi a kokarin da ake yi na maido da gwamnatin da kasashen duniya su ka amince da halaccinta - wanda zai hada da amfani da hanyoyin siyasa da kuma taimakawa farar hula.

To amma jami'an na Saudiyya su ka ce sojojin taron dangin za su cigaba da hana dakarun Houthin kai-komo a Yemen, kuma idan ta kama ma, ana iya dawo da hare-haren jiragen saman a kowane lokaci.

Kasar Iran, wadda ake kyautata zaton ita ke samar da makamai ma 'yan Houthin, ta bayyana sanarwar da Saudiyya ta bayar da cewa wani cigaba ne a kokarin da ake na warware rigimar a siyasance.

Ta kuma yi maraba da kawo karshen, abin da ta kira, kashe-kashen farar hulan da ba su da wata kariya.

Wani harin jirgin saman da Saudiyya ta kai kan wani wurin ajiyar makaman 'yan tawayen da ke daura da Sana'a, babban birnin kasar ranar Litini, ya hallaka mutane akalla 38 tare da lalata gidaje da dama.

A halin da ake ciki kuma, jirgin ruwan dakon jiragen saman Amurka mai suna USS Theodore Roosevelt na dannawa zuwa mashigar ruwan Aden daura da gabar Yemen a jiya Talata. Jirgin zai hadu da wasu jiragen ruwan Amurka na yaki don tabbatar da cewa wannan yakin bai katse mahimman hanyoyin sufurin ruwa ba.

Jami'an gwamnatin Amurka sun karyata zargin cewa an tura jiragen ruwan ne don su kama jiragen ruwan Iran da ake tsammanin su na kai makamai ga 'yan Houthi.

XS
SM
MD
LG