Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

YEMEN: Kungiyar al-Qaida Ta Kwace Tashar Jirgin Sama dake Mukalla


Mayakan al-Qaida

Rikicin kasar Yemen sai kara rincabewa yake yi inda kungiyar al-Qaida ke kwace wasu wurare masu mahimmanci.

Mayakan al-qaida sun kwace ikon wata muhimmiyar tashar jirgin sama a birnin Mukalla dake kudancin Yemen, inda mayakan suka sami galaba.

Jami’ai sun ce, mayakan al-Qaida sun fuskanci ‘yar tirjiya daga sojoji jiya a Mukalla, wani birnin tashar jirgin ruwa dake birnin Hadramawt dake lardi mafi girma a Yemen.

Wata babbar matattarar mai dake kudancin Yemen ma ta fada hannun mayakan.

A farkon wannan watan mayakan al-Qaida suka kwace ikon wani sansanin soja a Mukalla. Sun kuma fasa wani gidan yari a birnin suka saki fursunoni dari uku.

Gumurzun da ake yi tsakanin dakarun hadin guiwa a karkashin jagorancin Saudi Arabiya da ‘yan tawayen Houthi ya bar gibi a wadansu sassan kasar musamman a gabar tekun kudancin kasar da kungiyar al-Qaida take yunkurin cikewa.

XS
SM
MD
LG