Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shahararren Dan Wasan Kwallon Kafa Diego Maradona Ya Mutu


Maradona
Maradona

Fitaccen dan wasan kwallon kafa Diego Maradona ya mutu bayan fama da matsalar bugun zuciya, a cewar mai magana da yawunsa.

A shekarar 1986, Mardona dan shekara 60 ya jagoranci Argentina a matsayin kaftin har suka yi nasarar lashe Kofin Duniya na World Cup.

A farkon wannan watan ne, aka samu nasarar yi masa tiyatar kwakwalwa a wani asibitin kwararru mai zaman kansa a Buenos Aires, babban birnin Argentina.

Gwarzon dan kwallon na Argentina ya mutu a gida, makonni uku kacal bayan tiyatar da aka masa.

Maradona
Maradona

Rabon da ya bayyana a bainar jama'a tun ranar bikin haihuwarsa da ya cika shekara 60 a karshen watan da ya gabata kafin karawar da kungiyarsa ta yi da Patronato.

Tsohon dan wasan na kungiyar Napoli, da Barcelona da kuma Boca Juniors ya sha jinya a asibiti tsawon shekaru, galibi saboda salon rayuwarsa.

An kwantar da shi a asibiti a cikin watan Janairun shekarar 2019. Ya kuma yi rashin lafiya a Gasar cin Kofin Duniya na shekarar 2018 a Rasha, inda aka dauki hoton bidiyon lokacin da ya sume a cikin akwatin zartarwa a wasan Argentina da Najeriya.

An kai Maradona asibiti a shekarar 2004 bayan da ya yi fama da tsananin ciwon zuciya da matsalolin numfashi da ke da nasaba da amfani da hodar iblis. Daga baya aka kai shi asibitin kula da masu shan kwayoyi a Cuba da Argentina kafin a yi masa tiyata a shekarar 2005 don taimaka masa ya rage kiba.

A shekarar 2007 ya kai kansa zuwa asibitin Buenos Aires don a taimaka masa shawo kan matsalar shan barasa.

Diego Maradona 1960-2020
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:07 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG