Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shan Kayan Maye Ke Haddasa Yawan Hadurra a Abuja - Hukumar FRSC


Road safety officers help to carry a hose at the scene of the fire which broke out at the headquarters of the Nigeria Football Federation in Abuja, August 20, 2014.
Road safety officers help to carry a hose at the scene of the fire which broke out at the headquarters of the Nigeria Football Federation in Abuja, August 20, 2014.

Hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta Najeriya wato FRSC ta bayyana cewa karuwar hadurra da ake gani na da alaka da tu’amalli da ababen maye a bangaren direbobi musamman a kwanakin karshen mako.

Hatsarin da ya hada motoci biyu a birnin tarayya Abuja a mahadar unguwar Life Camp ya sanya wasu shaidu fantsama kan titin don taimakawa wadanda al’amarin ya rutsa da su kafin isowar jami’an hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta FRSC wurin.

Ana dai samun karuwa a yawan hadurra musamman a manyan titunan birnin tarayya Abuja, lamarin dake kara ta’azzara inda ya kai ga masu ruwa da tsaki a Najeriya kamar yan majalisar wakilai, bayyana matukar damuwarsu a kai sakamakon yadda ake rasa rayuka da dukiya.

Wani direba mai suna, Mukhtar Nasir, ya ce wani dan uwansa mai tukin mota ya saci hanya a wata unguwa a Abuja, ya yi sanadiyar hatsarin da ya sanya shi rasa yatsan shi, a baya-bayan nan kuma lamarin ya matukar sanya shi cikin mummunan yanayi.

Jami’i a sashen wayar da kan al’umma na hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta kasa wato FRSC dake birnin Abuja, Muhammad Kabir Abubakar, ya ce kari a yanayin hadurra da ake gani musamman na baya-bayan nan a kan titunan unguwanni kamar su Life camp, Wuse, area 1, Gwarimpa, Kugbo da dai sauransu, ba ya rasa nasaba da tu'amalli da kayan maye da wasu direbobi ke yi a akasarin lokuta a karshen mako daga ranar Juma'ah zuwa Lahadi.

Muhammad Kabir Abubakar ya kara da cewa hukumar FRSC na yin duk mai yiyuwa wajen rage yawan hadurra a kan titunan Najeriya kamar yin amfani da na'urorin zaman wajen gano idan direba ya yi tuki cikin maye, a dauki matakan da suka dace.

Auwal Musa Kontagora, jami’in hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Najeriya wato VIO ya bayyana cewa dole ne a koma kan teburin duba tsarin bada lasisi kamar na da da ake bayar da lasisi na gajeren zango, wato duk wata uku a sabunta hakan har sau uku, ya zama watanni 9 kafin baiwa mutum lasisi na dindindin.

A cikin mafita da ake ganin za su taimaka wajen rage da kuma kawo karshen yawan hadurra da ake gani a duk fadin kasar, sun hada da bin ka’idoji tuki, da rage gudu fiye da kima, koyon tuki na akalla tsawon watannin 9 kafin mutum ya sami lasisi da dai sauransu kamar yadda masu ruwa da tsaki suka bayyana.

XS
SM
MD
LG