Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tankar Mai Ta Hallaka Mutane 9 a Tsakanin Lagos da Ibadan


Wasu cikin motocin da suka kone
Wasu cikin motocin da suka kone

Tankar man fetur da ta fadi saboda lalacewar birki a hanyar Lagos zuwa Ibadan ta yi sanadiyar mutuwar mutane tara, kuma motoci fiye da 50 sun kone kurmus.

Hukumomi sun tabbatar mutane tara ne suka rasa rayukansu yayin da motoci fiye da 50 suka kone sakamakon faduwar da wata tankar mai ta yi.

Hadarin ya auku ne a lokacin da birkin motar dake shake da man fetur ya lalace, sai motar ta fara komawa baya baya har ta fara karo da motocin dake binta.

Mr. Ameje shi ne babban kwamandan hukumar kula da haduran motoci ta Najeriya wato, FRSC, na reshen jihar Lagos ya ce bayan da kura ta lafa sun kirga akalla motoci 54 da suka kone kurmus kana sun gano gawarwakin mutane tara da suma suka kone ba’a iya ganesu.

Shugaban hukumar dake bada agajin gaggawa na jihar Lagos Mr. Adeshina Timiyu, yace akwai mutane biyu da aka kai asibiti dake samun kulawar likitoci.

Wani direban tankin mai Ibrahim Dogon Kyerap ya dora alhakin irin wannan hadarin ne akan direbobin tankuna ko kuma manyan motoci a kasar. Yana cewa direbobin zasu san motar bata da lafiya amma sai su ce zasu lallaba haka nan. Sai ya je ya yi lodi ya tafi. Idan mota bata da birki yaya za’a sata kan hanya?

Tuni dai hukumomin bada agajin gaggawa da kuma kiyaye haduran mota suka fara aiki gadan gadan na kwashe motocin da suka kone domin motoci da sauran jama’a su ci gaba da wucewa.

A saurari rahoton Babangida Jibrin da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG