Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shari'ar Tsige Trump Karo Na Biyu Na Ci Gaba A Yau Asabar


Shari'ar tsige Trump.
Shari'ar tsige Trump.

Majalisar dattawan Amurka ta ci gaba da zama da safiyar yau Asabar a matsayin kotu a kan batun tsige tsohon shugaban kasa Donald Trump.

Tsakanin masu shigar da kara daga majalisar wakilai da lauyoyin Trump babu wanda ya bayyana niyar gabatar da shaidu, lamarin dake nuni da bangarorin guda biyu zasu kawo karshen mahawarar su a yau Asabar. Kana bada bata lokaci ba kada kuri’a ta biyo baya.

A ranar Juma’a, lauyoyin Trump sun kammala bayyana kariya da suke baiwa tsohon shugaban na Amurka, inda suka musanta cewa ya ingiza taron jama’a su kai mummunar hari a kan majalisar dokoki a ranar shida ga watan Janairu. Lauyoyin Trump sun kwatanta wannan shari’a da wani bita da kullin siyasa ce kawai.

Lauyoyin Trump sun bada bahasin su ne a cikin sa’o’I uku a ranar Juma’a, amma basu yi amfani da sa’o’I 16 da aka basu su gabatar da bayanan su.

Lauyoyin Trump sun fadawa sanatocin cewa tsohon shugaban kasar nada hurumin kalubalantar rashin nasarar da ya yi a karawar sa da Joe Biden kana jawabin Trump na mintoci 70 kafin tarzomar ta ranar shida ga watan Janairua kan majalisar dokokin, bai kai matsayi da za a kira shi da ingiza tashin hankali ba.

Lokacin da Trump ya gargadi dubban magoya bayansa da su tashi su kwato ma kansu ‘yanci to “koda da fada ne”, masu kare shi sun ce wadannan kalaman daidai suke da irin kalaman da ‘yan Democrat suka yi a baya da suka haddasa tashin hankali.

Lauyoyin Trump sun saka hotunan bidiyo dake nuno wasu kusoshi na jami’iyar Democrat, ciki har da mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris da Elizabeth Waren da kuma shugaban ‘yan Democrat a majalisar dattawa Schuck Schummer, inda suka yi amfani da kalamar fada ba tare da wani muhalli ba.

XS
SM
MD
LG