Da ta ke jawabi a Frankfurt, kasar Jamus, Lagarde ta ce, "tattalin arziki ya yi ta tafiyar hawainiya na lokaci mai tsawo," ta yadda mutane da dama ba su amfana, da kuma kafa tushen "matsalolin zamantakewa da siyasa a kasashe da dama."
Ta kuma zayyana kalubalolin da za a fuskanta a kasashen da su ka ci gaba, ciki har da karfin da dala za ta yi har ta jinkirta bunkasar tattalin arziki a Amurka, da jinkiri wajen saka jari da kuma rashin ayyukan yi a kasashen da ke amfani da takardar kudin Euro, da kuma tangal-tangal da tsadar kaya da za a fuskanta a kasar Japan.
To amma Lagarde ta kuma zayyana wasu kasashen da ta ce fa'ida na nan tafe. Kasar Indiya, in ji ta, na da karfin cigaba da mikewa da kuma samun karin kudaden shiga. A yankin kudancin Asiya kuwa, kasashe irinsu Indonesia, da Malaysia da Philippines, da Thailand da Vietnam na "kokari," a cewar Lagarde.
Shawo Kan Kalubalen Tattalin Arzikin Duniya

Shugabar Asusun Lamuni na Duniya (IMF), Christine Lagarde, ta fadi yau Talata cewa ya kamata duniya ta hada kai don shawo kan kalubalolin tattalin arziki, ciki har da tafiyar hawainiya da tattalin arziki ke yi, da faduwar farashin kaya da kuma tsuke bakin aljuhun da gwamnatoci da dama ka yi nan gaba.
WASHINGTON, DC —
Labarai masu alaka
Maris 25, 2023
An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
Maris 25, 2023
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
Maris 25, 2023
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 26, 2023
Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris Ta Isa Ghana
-
Maris 21, 2023
Saudiyya Ta Ce Ranar Alhamis Watan Azumi Zai Kama
-
Maris 17, 2023
Kotun ICC Ta Ba Da Izinin Kama Putin
-
Maris 13, 2023
Shugaba Buhari Ya Taya Xi Jinping Murnar Sake Lashe Zabe