Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shehun Borno Ya Kira Al'ummar Jihar Su Yi Addu'a da Azumin Kwana Uku


Shehun Borno Alhaji Umar Garbai El-Kanemi

Ganin yadda 'yan kungiyar Boko Haram ke kai hari suna hallaka rayukan jama'a ya sa Shehun Borno Alhaji Umar Garbai El-Kanemi ya kira al'ummar musulmi dake jihar su soma addu'a da azumin kwana uku daga yau.

Manufar addu'a da azumin da Shehun Borno ya kira jama'ar musulmi su soma yau shi ne a roki Allah ya kawo karshen hallaka jama'a da dukiyoyinsu da 'yan Boko Haram ke yi.

Shehun yace yanayin ya jefa jama'a da dama cikin damuwa yayin da ake cigaba da samun kwararowar mutane da suka gudo daga kauyukan da maharan suka mamaye. Ya kira musulmai su roki Allah domin kubutar da jama'a daga bala'in da suke ciki.

Kiran ya fito ne daga wata sanarwar da ta fito daga fadar Shehun dake dauke da sa hannun sakataren fadar Alhaji Zanna Lesu. Wakilin Muryar Amurka ya nemi karin haske daga sakataren wanda kuma yace yadda 'yan kungiyar Boko Haram suka kara tursasa jama'a suna kwararowa cikin Maiduguri ya sa suka tashi domin a kara rokon Allah. Yace tun ba yau ba suke ta rokon Allah amma Shehu ya ga abun na tsananani da yawa dalili ke nan yasa ya kira al'ummar jihar gaba daya da duk wani dan Najeriya dake da niyar taimako ya shiga azumin nan na kwana uku daga yau Alhamis.

Ban da haka a duk masallatan unguwoyi a dinga taruwa ana addu'a. Wadanda Allah ya budewa hanya su dinga yin sadaka kullum har a ga bayan ta'adancin 'yan Boko Haram. Musamman ana son a tallafawa wadanda suke sansanin 'yan gudun hijira da wadanda suke zaune cikin gidajen mutane.

Shehun ya kira kiristoci su ma su cigaba da yin addu'a Allah ya kawo karshen masifar da ta addabi jihar da kasa gaba daya.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00
Shiga Kai Tsaye


XS
SM
MD
LG