Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Da Gaske Dan Sanda Ya Tarwatsa Kansa Da Gurneti A Jihar Ebonyi?


Wani dan sandan Najeriya a lokacin da mabiya mazhabar Shi'a ke zanga-zanga a Abuja a shekarar 2018.

Rundunar 'yan sandan Najeriya a Jihar Ebonyi ta mayar da martani kan jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta, da ke cewa wani jami'inta ya yi kunar bakin wake ta hanyar tarwatsa kansa da bam a jihar Ebonyi.

Kakakin rundunar 'yan sandan ta Jihar Ebonyi da ke kudancin Najeriya Loveth Odah, ya bayyana cewa jami'in da lamarin ya rutsa da shi mai suna Idi Aminu, dan sanda ne mai mukamin Sifeto a karamar hukumar Afikpo ta Arewa, kuma lamarin ya faru ne a bisa kuskure.

Marigayi dan sandan ya danna hancin gurnetin da ke jikinsa ne a bisa kuskure, abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take ba tare da jikkata kowa ba, a cewar Odah.

Wani ganau dake zaune a yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa wata kafar yada labarai cewa mutane a yankin sun shiga rudani bayan aukuwar lamarin inda har yanzu haka ake zaman dar-dar.

Ya ce akasarin kamfanonin da ke yankin sun rurrufe dan gudun abin da ka iya biyo baya.

Karin bayani akan: Loveth Odah, Jihar Ebonyi, Usman Alkali Baba, IPOB, Nigeria, da Najeriya.

Idan ana iya tunawa, wannan ba shi ne karon farko ba da jami’in tsaro zai danna hancin gurneti bisa kuskure, lamarin da a yawancin lokaci ke yin sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Masana dai na ci gaba da yin kira ga hukumomin tsaro su kara kaimi wajen horar da jami’ansu a fannin amfani da makaman aiki, domin gujewa yawaitar faruwar irin wannan lamarin a gaba.

XS
SM
MD
LG