Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Jirgin Yakin Saman Najeriya Faduwa Ya Yi?


Daya daga cikin Jirgen yakin sama na Najeriya.
Daya daga cikin Jirgen yakin sama na Najeriya.

Kwana biyu bayan bata dabo da jirgin saman yakin Najeriya ya yi a yankin jihar Borno da ke arewa masa gabashin Najeriya, har yanzu ba a gano inda jirgin yake ba, wanda ke dauke da matuka biyu.

Sai dai wata sanarwa da rundunar sojin saman ta fitar a ranar Juma'a, ta ce akwai alamu da ke nuna cewa jirgin nata faduwa ya yi.

Jirgin na daga cikin Jirgin Yakin Najeriya da ke gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya, a yakin da kasar ke yi da kungiyar Boko Haram.

An daina jin duriyar jirgin mai lamba NA475 bayan da na’urar da ke bibiyar jirage ta daina ganinsa yayin da yake dauke da matuka biyu.

Jirgin ya bata ne a ranar 31 ga watan Maris.

Karin bayani akan: Boko Haram, Jirgin Yakin Saman na Najeriya, jihar Borno​, Sojojin Najeriya, Nigeria, da Najeriya.

“Amma ba a san mene ne musabbabin hatsarin ba da kuma inda matukan jirgin biyu suke.” Wata sanarwa da rundunar sojin saman Najeriyar ta fitar a shafin Twitter dauke da sa hannun darektan yada labarai, Air Commodore Edward Gabket ta ce.

“Matuka jirgin sun hada da Flight Lieutenant John Abolarinwa da Flight Lieutenant Ebiakpo Chapele.” Gabkwet ya kara da cewa.

Sanarwar ta kuma ce, jiragen sintirin rundunar da kwararru na musamman, suna can suna ci gaba da ayyukan nema da ceto tare da hadin gwiwar dakarun kasan Najeriya.

“A daidai wannan gaba, rundunar sojin Najeriya, ba ta cire tsammanin cewa komai zai iya faruwa ba, dangane da abin da ya shafi batan jirgin,” tana mai kyautata tsammanin cewa “nan ba da jimawa, za a gano inda matukan suke a kuma cece su.”

A ranar 21 ga Fabrairu, wani jirgin saman Najeriya dauke da sojoji bakwai ya fadi a kusa da filin tashin jirage na Abuja. Jirgin na kan hanyarsa ne ta zuwa jihar Neja, don neman daliban Kagara da aka sace.

Duka sojoji bakwai da ke cikin jirgin sun mutu.

A watan da ya gabata fadar shugaban kasar ta ce shida daga cikin jiragen sama na yaki 12 da aka yi cefanensu daga Amurka, za su isa kasar a tsakiyar watan Yuni.

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG